IQNA

Mayar Da Gasar Kur’ani Mataki Uku Ya Kayatar Da Mahalarta Matuka

15:00 - June 25, 2012
Lambar Labari: 2354146
Bangaren kur’ani, a wannan karon an mayar da gasar karatun kur’ani gami da harda da aka gudanar a matsayi na kasa da kasa a birnin Tehran karo na 29 zuwa matakai uku wanda kuma hakan ne ya kara fito da gasar fiye da sauran shekarun baya kamar yadda mahalarta daga kasashen ketare suka bayyana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa cewa a wannan karon an mayar da gasar karatun kur’ani gami da harda da aka gudanar a matsayi na kasa da kasa a birnin Tehran karo na 29 zuwa matakai uku wanda kuma hakan ne ya kara fito da gasar fiye da sauran shekarun baya kamar yadda mahalarta daga kasashen ketare suka bayyana ga manem alabarai.
Wannan dai shi ne karo na 29 da ake gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki a birnin Tehran a kowace shekara da nufin kara daukaka matsayin kur’ani ga sauran al’ummomin duniya sanin irin sako mai tsarki da yake da shi ga al’ummomin duniya, wanda manzon tsira annabin rahma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka ya zo da shi.
A wannan karon an mayar da gasar karatun kur’ani gami da harda da aka gudanar a matsayi na kasa da kasa a birnin Tehran karo na 29 zuwa matakai uku wanda kuma hakan ne ya kara fito da gasar fiye da sauran shekarun baya kamar yadda mahalarta daga kasashen ketare suka bayyana masu daukar labarai na kamfanin dilalncin labaran kur’ani mai tsaki na iqna a wajen taron.
1036565

captcha