IQNA

Zaman Taro Kan Bayar da Kariya Ga Masallacin Qods A kasar Birtaniya

16:06 - June 25, 2012
Lambar Labari: 2354205
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taro na kwamitin kare masallacin Qods da ke da babbar cibiyar abirnin London fadar mulkin kasar Birtaniya tare da halartar masana daga sassan kasar da kuma musulmi gami da palastinawa mazauna kasar wadanda suka nuna goyon bayansu ga duk wani matki na kare masallacin Qods.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI cewa, acikin wannan makon an gudanar da zaman taro na kwamitin kare masallacin Qods da ke da babbar cibiyar abirnin London fadar mulkin kasar Birtaniya tare da halartar masana daga sassan kasar da kuma musulmi gami da palastinawa mazauna kasar wadanda suka nuna goyon bayansu ga duk wani matki na kare masallacin Qods mai alfarma daga yunkurin yahudawan sahyuniya.
Irin yadda masu kishin islama suka kai ga madafun iko a wasu kasashe na larabawa da su kai fama da rikici har ya kia ga kawo karshen shugabanninsu hakan ya mayar da hannun agogo baya a jankoron haramtacciyar kasar Isra’ila kan al’ummomin yankin, musamman a gabas ta tsakiya da arewacin Afirka.
Ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da aka fara bore a kasar Tunisia wanda shi ne bore na farko da aka yi a kasashen larabawa da kai ga ballewar sauran tashe-tashen hankula a yankin baki daya, daga lokacin hantar haramtacciyar kasar Isra’ila ta kada, domin kuwa ta sani sarai cewa, hakan ba zai zama maslaha gare ta a nan gaba ba.
Masanin ya ce ya imanin cewa irin yadda masu kishin islama suka kai ga madafun iko a wasu kasashe na larabawa da su kai fama da rikici har ya kia ga kawo karshen shugabanninsu hakan ya mayar da hannun agogo baya a jankoron haramtacciyar kasar yahudawa ga kasashen larabawa da na musulmi. 1036541
captcha