Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrwa na yannar gizo cewa, karamin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci ta Iran a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa ya sanar cewa mai yiwuwa ya shirya gudanar da wani zaman taro kan rikicin siyasar da yaki karewa a kasar Syria da nufin kara jawo hankulan bangarorin rikicin zuwa ga fahimtar juna da sulhu a tsakanin bangarorin biyu.
Masu aiki a shafin yanar gizo sun mayar da martani kan ministan harkokin cikin gida na kasar Faransa kan wasu kalamai nasa na kyamr musulunci da yin batunci ga mabiya addinin muslunci da ya yi a cikin ‘yan lokutanan wanda kuma ba shi ne karon farko da ake samun irin hakan ba a tsakanin manyan jami’an gwamnatin kasar Faransa.
A cikin shekarar da ta gabata ma shi kansa shugaban kasar ya fito babu kunyar Allah balantana ta mutane, ya yi kalamai na batunci kan addinin muslunci, kuma ya soki mabiya wannan adini da suke a kasar, duk kuwa da cewa a halin yanzu addinin muslunci shi ne addni na biyu ta fuskacin yawan mabiya a kasar faransa, duk kuwa da cewa har inda yau take gwanbatin kasar ta ki amincewa da shi a matsayin daya daga cikin addinan kasar.
A matakin aikin safke wajibi da ke kansu, masu aiki a shafin yanar gizo sun mayar da martani kan ministan harkokin cikin gida na kasar Faransa kan wasu kalamai nasa na kyamr musulunci da yin batunci ga mabiya addinin muslunci da ya yi a cikin ‘yan lokutanan wand ake bayyana hakan a matsayin wani mataki na nuna wariya ga musulmi. 1036304