IQNA

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Ta Bayar Da Labari Kan Karancin Ruwa A Gaza

22:27 - June 25, 2012
Lambar Labari: 2354344
Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta bayar da labari kan matsananciyar matasalar karancin ruwan sha a yankin zirin Gaza inda palastinawa suke fama da matsaloli sakamakon killacewar da yahudawan sahyuniya suke wa yankin tun kimanin shekaru shida da suka gabata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta bayar da labari kan matsananciyar matasalar karancin ruwan sha a yankin zirin Gaza inda palastinawa suke fama da matsaloli sakamakon killacewar da yahudawan sahyuniya suke wa yankin tun kimanin shekaru shida da suka gabata ba tare da wat akasa daga cikin yammacin turai ko karnukan farautarsu daga cikin larabawa sun ce uffan kan hakan ba.
Haramtacciyar kasar Isra’ila ce take amfana da salon siyasar dabbanci da wawanci da wuce gona da iri ta mabiya tafarkin salafiyya da suke cikin gwamnatin kasar Masar a halin yanzu inda suke bata sunan muslunci da bakanta fuskarsa da siyasara mai tsarki a idon duniya kamar yadda kowa ya gani a cikin ‘yan watanni da suka yi mulki.
A kasar Jamus kuwa ministan harkokin cikin gidan kasar ne ya yi kakkausar suka kan mabiya tafarkin salafiyya dangane da abubuwan da suke yi a kasdar na wuce gona da iri da sunan cewa suna bin tafarkin addinin mulsunci ne da kuma rarraba kur’anai a tsakanin al’ummar kasar ta Jamus.
A bangare guda kuma ana shirin gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci na kasar baki daya, wanda kuma ake ganin zai amfani matuka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Jamus na da musulmi da yawansu ya haura miliyan hudu a fadin kasar, saboda haka wannan jami’a ta dauki nauyin bayar da karatu kan muhimman abubuwan da ya kamata masu jagorancin masallatai su koya kafin fara limanci, wanda kuma malaman addinin muslunci ne za su koyar da su a jami’a bisa tsari na karatun digiri.
1036564

captcha