IQNA

Masu Kishin Islama Ne Suka Lashe Zaben Shugaban kasar Masar Zagaye Na biyu

22:24 - June 25, 2012
Lambar Labari: 2354347
Bangaren kasa da kasa, masu kishin islama ne suka lashe zaben shugaban kasa zagaye na karshe da aka gudanar a kasar Masar a cikin wannan mako kamar dai yadda hukumar zabe zaman kanta ta kasar Masar din ta sanar jiya a lokacin da shugaban hukumar yake gabatar da jawabi dangane da sakamakon karshe na zaben.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, daga karshe dai masu kishin islama ne suka lashe zaben shugaban kasa zagaye na karshe da aka gudanar a kasar Masar a cikin wannan mako kamar dai yadda hukumar zabe zaman kanta ta kasar Masar din ta sanar jiya a lokacin da shugaban hukumar yake gabatar da jawabi dangane da sakamakon karshe na zaben wanda ya samu karbuwa.
A labari na daban kuma an habarta cewa jam’iyun adawa uku na masu kishin islama a kasar Algeria sun sanar da kafa wata babbar hadaka domin fuskantar zabuka masu a kasar da nufin kayar da jamiyya mai mulki a halin yanzu a kasar karkashin jagorancin shugaba Butaflika.
Wadannan jamiyu wadanda suka shafe tsawon lokaci suna adawa sun samu dama a wannan lokaci da ake bore a cikin wasu kasashen larabawa domin kawar da gwamnatoci ‘yan kama karya da suke yin amshin shata ga Amurka, misali daga ciki kuwa shi ne abin da ya faru akasar Masar, inda aka kawar da tsohon shugaban mulkin kama karya dan koren Amurka, kuma masu kishin islama suka mamaye sha’ann mulki.
jam’iyun adawa na masu kishin islama a kasar Algeria sun dai sanar da kafa babbar hadaka ne domin fuskantar zabuka masu a kasar da nufin kayar da jamiyya mai mulki, duk kuwa da cewa masu kishin islama da suka samu mulki a Tunisia da Libya sun bayan da mummnan misali, inda suka mika kai ga turawan yamma.
1036499


captcha