Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa: sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun sanar da wani maummunan mataki da suke son dauka a yankunan da suke ci gaba da mamayewa na Kudus da yammacin kojin jodan inda suke yi masu barazanar rusa masu gidaje. Majiyar labarai ta Palestine Info ne ta watsa wani rahoto da ke bayyana cewa; tuni aka rusa da lalata gidaje biyar a garin Silwan da ke kuduncin masallacin kudus mai tsarki kuma hakan yana nuni yadda sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da siyasarta ta nuna wariya da mummunan aiki da ta saba na takurawa pararen hula Palsdinawa da ba su san hawa ba balantana sabka kuma daidai lokaci guda kungiyoyi na kasa da kasa da hukumomi na duniya sun yi gum da bakinsu bas u cewa komi kan wannan mummunan aiki na Haramtacciyar kasar Isra'ila.
1037666