IQNA

Iran Na Kokarin Ganin An kauce Ma Kashe Fararen Hula A Rikicin Kasar Syria

17:54 - June 26, 2012
Lambar Labari: 2355181
Bangaren siyasa, mataimakin baban kwamandan askaraan kare juyin juya halin muslunci a Iran Janar Mas'ud Jazairi ya bayyana cewa kasar Iran na yin iyakacin kokarinta domin ganin cewa rikicin da ke faruwa akasar Syria bai yi sanadiyar mutuwar mutane fararen hula dab a su da hannu a rikicin ba tare da fatan ganin an warware shit a hanyoyi na zaman lafiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, babban mataimakin baban kwamandan askaraan kare juyin juya halin muslunci a Iran Janar Mas'ud Jazairi ya bayyana cewa kasar Iran na yin iyakacin kokarinta domin ganin cewa rikicin da ke faruwa akasar Syria bai yi sanadiyar mutuwar mutane fararen hula dab a su da hannu a rikicin ba tare da fatan ganin an warware shit a hanyoyi na zaman lafiya da lumana.
A wani labarin kuma a daidai lokacin da kungiyar tsaro ta kasashen yammacin turai ke shirin gudanar da wani taro don tattauna batun harbo jirgin saman yakin kasar Turkiya da sojojin Siriya suka yi, kasar Siriyan ta ja kunnen kungiyar kungiyar tsaro ta kasashen yammacin turai da ta guji hada baki da kasar Turkiyya wajen ci gaba da kulla makarkashiya ga kasar.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Siriya Jihad Makdisi ya bayyana cewar jirgin yakin na Turkiya samfurin F-4 ya keta hurumin kasar Siriya ne don haka sojojin kasar suka harbo shi a matsayin mataki na tsaron kasa.
Makdisi ya kara da cewa idan har taron don kwantar da rikicin da ya ke kokarin kunno kai tsakanin kasashen biyu ne, to suna maraba da shi da kuma yi masa fatan alheri, amma idan har da nufin kulla makarkashiya ga kasar Siriya ne to muna sanar da su cewa sararin samaniyar kasar Siriya dai hakki ne na kasar kamar yadda sararin samaniyar Turkiya hakkin ne na kasar don haka Siriya za ta yi duk abin da za ta iya wajen kare mutumci da kuma tsaron kasarta.
1037375


captcha