IQNA

Saka Hannayen Jari A Cikin Harkokin Kasuwanci Na Da Matukar Muhimmanci Ga Kamfanonin Musulmi

17:54 - June 26, 2012
Lambar Labari: 2355185
Bangaren siyasa, daya daga cikin muhimman lamurra day a kamata musulmi su mayar da hankali kansu shi ne, kafa hanyoyi na kasuwanci das aka hannayen jari ta yadda hakan zai baiwa tattalin arzikin kasashen musulmi damar saar da wata hanya ta warware matsallinsu da suke fuskanta a matsayi na daidaiku ko kuma amatsayi na kasashe.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto aga shafin sadarwa na yanar gizo malam Khunsari yana cewa daya daga cikin muhimman lamurra day a kamata musulmi su mayar da hankali kansu shi ne, kafa hanyoyi na kasuwanci das aka hannayen jari ta yadda hakan zai baiwa tattalin arzikin kasashen musulmi damar saar da wata hanya ta warware matsallinsu da suke fuskanta a matsayi na daidaiku ko kuma amatsayi na kasashe da gwamnatoci.

Jam'iyya mai mulki a kasar Sudan ta yi kakkausar suka kan sanarwar da gwamnatin Amurka ta fitar da ke gargadin 'yan kasarta da suke Sudan dangane da halin da kasar take fuskanta na zanga zanga.
Jami'in watsa labarai a jam'iyyar National Congress Party da ke mulkin kasar Sudan Badruddin Ahmad Ibrahim a yau litinin ya bayyana cewa: Zanga zangar da al'ummar Sudan ke gudanarwa a birnin Khartum da wasu yankunan kasar, zanga zanga ce ta nuna rashin amincewa da siyasar gwamnati ta tsuke bakin aljihu da kuma matsalar tashin farashin kayayyakin abinci, don haka babu dalilin da zai sanya har wata kasa ta kai ga gargadin 'yan kasarta dangane da abin da ke faruwa a kasar ta Sudan.
Ahmad Ibrahim ya kara da cewa: Wannan mataki da gwamnatin Amurka ta dauka ba zai amfanar da kasar Sudan da matakan tsaro da sulhun duniya ba, kuma duk wanda ke rayuwa a birnin Khartum zai kai ga fahimtar cewa abin da ke faruwa bai kai matakin tsoma bakin gwamnatin kasar ba, ballantana wata kasa ta daban.
1037464




captcha