IQNA

Alkalan Gasar Kur'ani Na Kasa Da Kasa Na Iran Sun Yi Rawar Gani

17:54 - June 26, 2012
Lambar Labari: 2355186
Bangaren Kur'ani, alkalana gasar karatun kur'ani mai tsarki gami da harda da aka gudanar a mataki na kasa da kasa a jamhuriyar muslunci ta Iran sun taka gagarumar rawa wajen fito da matsayin gasar da kuma irin rawar da Iran din take takawa a duniya a wannan fage sabanin sekarun da suka gabata kafin samun nasarar juyin juya halin muslunci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar day a yi da daya daga cikin malaman addini kan gasar kur'ani karo na 29 ya sheda cewa alkalana gasar karatun kur'ani mai tsarki gami da harda da aka gudanar a mataki na kasa da kasa a jamhuriyar muslunci ta Iran sun taka gagarumar rawa wajen fito da matsayin gasar da kuma irin rawar da Iran din take takawa a duniya a wannan fage sabanin sekarun da suka gabata kafin samun nasarar juyin juya halin muslunci a cikin shekaru talatin da uku da suka gabata.

Kasar Saudiyya ta kasance a mataki na gaba a lokutan baya, amma daga baya ta yi kasa, ga shi kuma yanzu tun bayan sanarwar mutuwar yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Yarima Nayef bn Abdul'aziz wacce kuma ta zo a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar boren al'umma masu neman sauyi a bangarori daban-daban na kasar masharhanta suke ganin kasar Saudiyyar za ta shiga wani mawuyacin hali na dar-dar da rashin tabbas.
Masanan dai suna ganin mutuwar Nayef wanda ake ganinsa a matsayin tushe sannan kuma kanwa uwar gami wajen murkushe duk wani kokari na kawo sauyi a kasar Saudiyyan da ma wasu daga cikin kasashen larabawa musamman idan aka yi la'akari da irin rawar da ya taka wajen tura sojojin Saudiyya da kawayenta zuwa kasar Bahrain da kuma ci gaba da zaluntar al'ummar kasar masu neman sauyi ta sanya mahukuntan Saudiyya fuskantar kalulbale guda biyu manya wadanda su ne yadda za a ci gaba da fuskantar irin wannan bore na al'umma wanda ya iso har birnin Riyadh babban birnin kasar da kuma batun nada sabon yarima mai jiran gadon.
1033036



captcha