IQNA

Akasarin Mutanen Kasar masar suna fatan ganin an yanke alaka da Isra'ila

17:59 - June 27, 2012
Lambar Labari: 2356041
Bangaren kasa da kasa, akasarin mutanen kasar masar suna fatan ganin ahukuntan kasar sun yanke alaka da haramtacciyar kasar Isra'ila tare da kara fada wannan laka da sauran kasashen musulmi maimakon ika kai ga bakaken manufofi na siyasar yahudawa da kasashen yammacin turai da kasar take akai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, akasarin mutanen kasar masar suna fatan ganin ahukuntan kasar sun yanke alaka da haramtacciyar kasar Isra'ila tare da kara fada wannan laka da sauran kasashen musulmi maimakon ika kai ga bakaken manufofi na siyasar yahudawa da kasashen yammacin turai da kasar take akai a lokacin mulkin day a gabata.
Manyan fitattun 'yan siyasa na kasar Masar sun gudanar da wani zama da nufin kara matsa lamba kan tsohon shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya Muhamamd Baradei domin ya karbi mukamin pira ministan kasar.

Jaridar Yaum Sabi da ake bugawa a birnin Alkahira na kasar Masar ta bayar da rahoto a shafin na yanar gizo a yau cewa, 'yan siyasar sun gudanar da zaman ne a ofishin tsohon dan takarar neman shugabancin kasar Abdul mun'im Abul Futtuh, daga cikinsu kuwa har da wakilan kungiyar ikhwanul muslimin da kuma sauran jam'iyun siyasa daban-daban na kasar, inda suke ganin wajibi ne a matsa lamba kan Muhammad Baradei domin ya amince ya karbi matsayin pira minister, amma har yanzu yaki amincewa da hakan.

A bangare guda kuma har yanzu dubban mutane na ci gaba da yin zaman dirshan a dandalin Tahrir, domin neman majalisar sojin kasar ta fitar da hannun baki daya daga harkokin siyasar kasar.
1038887


captcha