IQNA

Mataimakin Shugaban Indonesia Ya Yi Kira Da A Rika Yin Tadabbur A karaun Kur’ani

21:59 - June 27, 2012
Lambar Labari: 2356115
Bnagaren siyasa da zamantakewa, mataimakin shugaban kasar Indonesia Budiono ya yi kira da a rika yin tadabbur a cikin karatun kur’ani mai tsarki maimakon karanta shi kawai ba tare da yin tunani kan abin da ayoyinsa masu tsarki suka kunsa ba domin kuwa hakan shi ne babban abin da ke sanya musulmi yin abin da ba shi a cikin addininsu saboda rashin sani ko kuma sakaci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa mataimakin shugaban kasar Indonesia Budiono ya yi kira da a rika yin tadabbur a cikin karatun kur’ani mai tsarki maimakon karanta shi kawai ba tare da yin tunani kan abin da ayoyinsa masu tsarki suka kunsa ba domin kuwa hakan shi ne babban abin da ke sanya musulmi yin abin da ba shi a cikin addininsu saboda rashin sani ko kuma sakaci wanda kuma a cewarsa, hakan shi ne babbar matsalar musulmi.
A cikin wannan makon an gudanar da zaman taro na kwamitin kare masallacin Qods da ke da babbar cibiyar abirnin London fadar mulkin kasar Birtaniya tare da halartar masana daga sassan kasar da kuma musulmi gami da palastinawa mazauna kasar wadanda suka nuna goyon bayansu ga duk wani matki na kare masallacin Qods mai alfarma daga yunkurin yahudawan sahyuniya.
Irin yadda masu kishin islama suka kai ga madafun iko a wasu kasashe na larabawa da su kai fama da rikici har ya kia ga kawo karshen shugabanninsu hakan ya mayar da hannun agogo baya a jankoron haramtacciyar kasar Isra’ila kan al’ummomin yankin, musamman a gabas ta tsakiya da arewacin Afirka.
Ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da aka fara bore a kasar Tunisia wanda shi ne bore na farko da aka yi a kasashen larabawa da kai ga ballewar sauran tashe-tashen hankula a yankin baki daya, daga lokacin hantar haramtacciyar kasar Isra’ila ta kada, domin kuwa ta sani sarai cewa, hakan ba zai zama maslaha gare ta a nan gaba ba.
1038653


captcha