IQNA

Dukkanin Dakarun Kasa Suna Shirye Su Bayar Da Kariya Ga Juyin Juya Halin Musulunci

13:56 - June 28, 2012
Lambar Labari: 2356329
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyana cewa dukaknin mutanen kasar Iran da suka da dakaru da ma'aikata dukkansua shirye suke bayar da kariya ga tsarin musulunci karkashin juyin juya halin muslunci da kasar ta yi domin rayuwa acikin karama da 'yanci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na yanar gizo cewa, Aytaollah Ozma Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyana cewa dukaknin mutanen kasar Iran da suka da dakaru da ma'aikata dukkansua shirye suke bayar da kariya ga tsarin musulunci karkashin juyin juya halin muslunci da kasar ta yi domin rayuwa a cikin karama da 'yanci da kuma 'yan adamtaka.
Yayin da ya ke jinjinawa Ayatullah Beheshti da abokan aikinsa da suka yi shahada a irin wannan ranar kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana kyautata ayyukan ma'aikatar shari'a da kuma tabbatar da adalci irin wannan tsarin Musulunci ya ke son cimma wani share fage ne na magance da dama daga cikin matsalolin da ake fuskanta da kawo karshen lalata da almundahana. Jagoran ya ci gaba da cewa: Bisa la'akari da irin karfi da damar da ake da su a kasar nan, ko shakka babu za a iya cimma wannan manufa na karfafa ma'aikatar shari'a ta hanyar kokari, samar da sabbin abubuwa da kuma amfani da irin karfin da ake da shi.
Haka nan kuma yayin da yake Karin haske kan abubuwan da ake bukata wajen karfafa ma'aikatar shari'ar, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: tsara wani tsari da shiri kammalalle wanda ya shafi dukkanin bangarori daya ne daga cikin mafiya muhimmancin ayyukan kyautata ma'aikatar shari'a.
Jagoran ya ci gaba da cewa: tsara ayyuka da ya kumshi dukkanin bangarori aiki ne mai matukar muhimmanci, to amma mafi muhimmanci sama da wannan shi ne aiki ba kama hannun yaro wajen aiwatar da wannan shiri a aikace.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: ma'anar aiki ba kama hannun yaro ba shi ne yin aiki ba tare da lura ba. A saboda haka wajibi ne a gudanar da aiki cikin hikima da lura, amma ba tare da jinkiri ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana nuna kwarewa wajen yanke hukumci na shari'a a matsayin daya daga cikin abubuwan da ake bukata wajen karfafa ma'aikatar shari'ar inda ya ce: Wajibi ne hukumcin da za a fitar ya zamanto ya dogara da hujjoji karfafa ta yadda idan da za a sake gabatar da hukumci a gaban kwararru na fikihu da shari'a, alkalin da ya yanke hukumci ba zai sami wata damuwa ba.
Har ila yau kuma yayin da ya ke jaddada wajibcin rage tura (masu laifi) gidajen yari a wajen hukumci a matsayin wata siyasa ta ma'aikatar shari'a, Jagoran cewa ya yi: Wajibi ne gwargwadon yadda za a iya a rage yanke hukumcin tafiya gidan yari, don kuwa gidan yari wani lamari ne ba abin so ba wanda kuma ya ke da matsaloli da yawa ga su kansu ‘yan fursunan da iyalansu kai hatta ma wajen aikinsu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce kiyaye mutumcin mutane daya ne daga cikin lamurra masu muhimmancin gaske yana mai cewa: abin bakin cikin shi ne cewa bangare mai girma na wannan lamarin ya samo asali ne daga yada jita-jitan wasu jaridu da shafukan internet. Bai kamata ma'aikatar shari'a ta tasirantu da irin wadannan farfaganda da jita-jita ba.
A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya bayyana hadin gwuiwa da aiki kafada da kafada tsakanin bangarori uku na gwamnati a matsayin daya daga cikin bukatun kasar Iran a wannan lokaci inda ya ce: A yau dai masu takama da karfi na duniya sun hada dukkanin karfinsu waje guda ko za su sami damar cutar da wannan tsari na Jamhuriyar Musulunci da kuma gagarumin yunkurinsa mai karfafa gwuiwan al'ummar duniyar musulmi.
Jagoran ya bayyana farkawar da al'ummar musulmi suka yi a wannan lokacin da kuma irin so da kaunar da suke nuna wa koyarwar Musulunci sakamako ne na yunkurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda ya sami gindin zama cikin zukatan al'ummar musulmi. Jagoran ya ci gaba da cewa: Duk wani ci gaba na ilimi da tsarin Musulunci zai samu, duk wani fitowar da al'ummar Iran za su yi kamar fitowarsu lokacin zabe da kuma tsayin dakan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a gaban ma'abota girman kan duniya, kowane guda daga cikin wadannan abubuwan lamari ne mai karfafa wa al'ummomi gwuiwa wajen ci gaba da neman ‘yancinsu karkashin inuwar koyarwa ta Musulunci. A saboda haka ne ma'abota girman kan suke amfani da dukkanin karfin da suke da shi a kan al'ummar Iran, ko za su sami damar kawar da su.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar dukkanin ihu bayan hari daban-daban da ake yi a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran musamman batun take hakkokin bil'adama da makamashin nukiliya don cimma wannan manufar ce don haka sai ya ce: Wadannan masu takama da karfi wanda suke kiran kansu kasashen duniya, suna ta kokari wajen ganin sun raba Jamhuriyar Musulunci ta Iran da al'ummarta.
Yayin da ya ke Karin haske kan wannan makircin kuwa, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Babban wadanda ma'abota girman kai su ke son cutarwa ta hanyar takunkumin da suke sanyawa su ne al'ummar Iran don matsin lamba ya sanya su mikewa da yin bore wa tsarin Musulunci. To amma cikin yardar Allah a wannan karon ma za su sha kashi, don kuwa har ya zuwa yanzu ba su fahimci al'umma da jami'anmu ba ne.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Al'ummar mu dai sun fahimci wannan yaudarar da kyaun gaske, a saboda haka ne al'umma suka kasance a dukkanin fagage, sannan kuma a hakikanin gaskiya jami'an gwamnati suna iyakacin kokarinsu.
Yayin da ya komawa kan kokarin da Amurka ta ke yi da dukkan karfinta wajen killace Jamhuriyar Musulunci ta Iran da mai da ita saniyar ware kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: A yau din nan suna cikin tsaka mai wuyan matsalolin da suka dabaibaye su sannan kuma suka gagara magance su, alhali kuwa Iran cikin ikon Allah tana da dukkanin abubuwan da take bukata.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar irin dukiya da albarkatun kasar da Iran take da shi da kuma mutane na kwarai da suka kware a fagage daban-daban bugu da kari kan rashin bashin duniya a matsayin daya daga cikin bangarorin karfin da Iran take da shi inda ya ce: A halin yanzu dai makiya sun shigo fage da dukkan karfinsu wajen hana Jamhuriyar Musulunci ta Iran ci gaba da amfanuwa da wadannan albarkatu, amma a bangare guda kuma jami'ai suna amfani da dukkanin karfin da suke da shi wajen kawo karshen wannan makarkashiyar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi dukkanin bangarorin gwamnatin da su hada kansu waje guda don aiki kafada da kafada wajen ciyar da kasar Iran gaba yana mai cewa duk wani abin da zai kawo rarrabuwa a tsakaninsu lamari ne da zai cutar da kasar Iran. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake jaddada wajibcin yarda da alkawarin Allah na taimakon dukkanin wanda ya yi kokari a tafarkin gaskiya.
1039656

captcha