IQNA

An Saka majami’ar Al-mahd Daya Daga Cikin Kayan Tarihi Na Duniya

15:52 - July 01, 2012
Lambar Labari: 2358442
Bangaren kasa da kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta majalisar dinkin duniya ta saka majami’ar l-mahd ta palastinu a matsayin saya daga cikin muhimman wurare masu tarihi na duniya lmarin da ya bakantawa haramtacciyar kasar yahudawa matuka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta majalisar dinkin duniya ta saka majami’ar l-mahd ta palastinu a matsayin saya daga cikin muhimman wurare masu tarihi na duniya lmarin da ya bakantawa haramtacciyar kasar yahudawa matuka kamar yadda jami’an haramtacciyar gwamnatin yahudawa sukayi ta furta kalamai kan hakan.
A nata bangaren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
Kungiyar ta hizbullah a kasar Lebanon ba ya ga kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar, ta kirayi iriin wadannan manafukan larabawa da su sake yin nazari kan makomarsu bisa la’akari da halin da ake ciki. 1040843
captcha