Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kwamitin daliban jami’an na kasashen musulmi ya kirayi shugaban kasar Masar Muhammad Mursi da ya fito karara ya bayyana matsayinsa dangane da haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma irin kisan gillar da ke wa palastinawa da kuma makomar alakarta da kasar Masar a lokacin mulkinsa kasantuwar cewa kasar tana dasawa da gwamnatin yahudawan a tsohuwar gwamnati.
Manzo Majalisar Dinkin Duniya da ya gudanar da bincike dangane da zargin tauye hakkokin Palasdinu da ake yi wa Haramtacciyar Kasar Isra'ila Richard Falk, ya zargi kasashen duniya da hada baki da wannan kasa maras halasci domin shimfida mummunar siyasar zalunci da kuma nuna wariyar jinsi a kan al'ummar Palasdinu.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya gabatar da jawabi a gaban wani zama na Hukumar Kare Hakkokin Bil'adama ta MDD a birnin Genewa a Yammacin jiya, Richard Falk ya ce yadda kasashen duniya masu fada-a-ji ke taka rawa wajen tunkarar matsalolin Palasdinu, wata alama ce da ke bayyana irin hadin bakinsu da HKI har ma aka kasa samar wa al'ummar Palasdinu da hakkokinsu.
Richard ya ce a yau dai ko shakka babu, al'ummar da ke rayuwa a yankin Gaza ba su da wata kariya a karkashin dokokin kasar da ake kira da suna Isra'ila, sannan kuma ya yi suka ga tsohon Firayi ministan kasar Birtaniya Tony Blair wanda shi ne shugaban bangarori 4 da aka dora wa alhakin samar da mafita ga rikicin 'Yan Sahyuniyya da kuma Palasdinu amma har yanzu ya kasa tabuka wani abin a zo a gani dangane da hakan.
1044027