Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Dr. Ali Akbar Velayati babban sakataren cibiyar fadakar muuslmi ta duniya ya fadi a gaban taron mata na duniya da ake gudanarwa kan fadakar musulmi cewa gwamnatocin duniya suna mahanga mabanbanta da kuma matakai da suke dauka kan haka daidai da yanayin kasashensu da kuma yunkurin al'umma, inda wasu suke bin matakai na hikima domin tunkarar lanarin, wasu suna amfani da karfi da hauka wajen murkushe al'ummarsu.
Jami'an Iran dai sun sha bayyana aniyarsu ta aiki tare da manyan kasashen duniyan wajen kawo karshen duk wani rashin fahimta da ya kunno kai a bangaren shirin nukiliyanta na zaman lafiya inda tsawon wadannan shekaru na tattaunawa ta tsaya kan wasu batutuwa guda uku a matsayin siyasarta a wannan fagen da suka hada da tsayin daka wajen tabbatar da hakkinta, amfani da hankali da girmama juna da kuma aiki a kas.
Dubi cikin tattaunawar baya-bayan nan tsakanin Iran da kasashen kungiyar 5+1 tun daga tattaunawar Istanbul na kasar Turkiya zuwa birnin Mosko na kasar Rasha ana iya bakar aniyar da manyan kasashen duniyar suke da ita kan Iran. A matsayin misali a tattaunawar farko ta birnin Istanbul, manyan kasashen duniya sun ki su amince da hakkin da Iran take da shi na amfani da makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya da Iran take da shi.
To amma sakamakon tsayin dakan Iran daga karshe dai a tattaunawar Istanbul ta biyu Madam Ashton din ta bayyana cewar manyan kasashen duniya za su girmama hakkin da Iran take da shi na mallakan fasahar nukiliya karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi NPT, haka nan kuma da aiki tare bugu da kari kan yin watsi da batun aiwatar da kudurin kwamitin tsaron MDD kan Iran a matsayin sharadin sake tattaunawa da Iran.
1049504