Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a yau bakin da suke halartar taron duniya kan fadakar al’ummar musulmi sun gana da jagoran juyin juya halin muslunci inda ya gabatar musu da jawabai dangane da matsayin wannan fadaka da ake shidawa a halin yanzu a cikin kasashen musulmi da na larabawa da kuma muhimmancin zama cikin fadaka dangane da yadda makiya muslunci suke kokarin ganin sun sace yunkurin musulmi domin kare manufofinsu na siyasa tare da kawar da hakinin manufar juyin al’umma.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kasashen yammaci ba su fahimci cewa ta hanyar sanya wa Iran takunkumi suna kara wa al'ummar kasar karfin gwuiwa ne wajen fada da duk wata barazana a kansu kamar yadda suka yi shekaru talatin da wani abin da suka wuce ba.
Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin ganawarsa da mahalarta taro na farko na kasa da kasa kan mata da farkawa ta Musulunci da ke faruwa da aka gudanar a Tehran inda ya ce tsaron shekaru talatin din da suka gabata al'ummar Iran sun tsaya kyam wajen fuskantar duk wani takuri daga makiya ta hanyar sadaukar rayuwarsu da dukiyoyin da ababen kaunarsu, wanda hakan ne ya sanya a halin yanzu Iran ta zamanto mai karfi sama da yadda take a da.
Yayin da ya koma kan rawar da mata suke takawa wajen ciyar da al'umma gaba da kuma farkar da al'umma, Jagoran ya ce rawar da suke takawa din rawa ce mai muhimmanci yana mai cewa duk wani yunkurin neman sauyi da mata suka shigo cikinsa to kuwa zai yi nasara.
A jiya ne dai aka kawo karshen wannan taron wanda ya sami halartar mata 1,500 daga kimanin kasashe 80 na duniya.
1050178