Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, Al-tuwaijari babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta kasashen musulmi ya bayar da shawarar tura malamai da masana musulmi daga kasashen duniya zuwa arewacin Mali domin ganawa da masu akidar kafirta musulmi da suke rusa kabruka da kuma masallatai gami da sauran wurare na tarihi da suke a wadannan rurare musamman a garin Tinbuktu mai tsihon tarihi.
A ci gaba da nuna damuwa da ayyukan da 'yan kungiyar nan ta Ansaruddeen masu tsaurin ra'ayi na rusa kabarurruka da wajaje masu tsarki na waliyai a garin Timbuktu na kasar Mali, al'ummar garin sun kafa wata kungiya ta dakarun sa kai don kare wadannan wajaje daga hare-haren 'yan Ansaruddeen din.
Yayin da yake sanar da kafa wannan kungiyar, shugaban dakarun Tahel Ould Sidi ya ce a halin yanzu sun kafa dakaru dauke da makami don hana kai hare-hare kan kaburburan waliyan. Tahel Ould Sidi ya kara da cewa ba za mu taba barin wadansu mutane wadanda ba su san komai a addini ba su ci gaba da rusa mana wajajen tarihinmu yana mai cewa babu inda Alkur'ani ya ce a rusa kabari.
Tun a watan Yunin da ya gabata ne 'yan kungiyar ta Ansardeen da aka ce tana da alaka da kungiyar Al-Qa'ida suka fara kai hare-hare kan kabarurrukan waliyan da rusa su suna masu shan alwashin rusa dukkanin irin wadannan kaburbura na waliyai ko da kuwa suna cikin masallatai ne.
Wannan aiki na 'yan Ansarudden din ya tada hankali cibiyoyi daban-daban na kasa da kasa lamarin da ya sanya har babbar mai shigar da kara a kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka Fatou Bensuda tace wannan aikin yana iya zama daga cikin laifuffukan yaki da za a iya hukumta masu aikata shi. Mutanen Timbuktun dai sun jima suna kiran da a kawo musu dauki don 'yantar da garin daga hannun 'yan wannan kungiya da a halin yanzu suke rike da garin.
1050292