Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a kasashe daban-daban al’ummar musulmi na ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna kyama kan matakin da mahukuntan gwamnatin wahabiyawan Saudiyya ta dauka na kame babban malami a gabacin kasar Shekh Namir wanda suka harbe shi da harsasan bindiga kuma a halin yanzu ba a san halin da yake ciki ba trun bayan kama shi.
A Lardin Qatif da ke gabacin kasar Saudiyya, dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gidan Sauratar Ali Saud tare kuma da yin kira da a gaggauta samar da sauyi a kasar ta hanyar shimfida salon mulki mai wakiltar al'umma a maimaikon daidaikun mutane 'yayan gidan sarauta da ke sarrafa kasar kamar dai yadda suka ga dama.
Duk da dimbin jami'an tsaron da aka jibge a yankin yau kusan shekara daya kenan, wannan bai hana wa masu zanga-zangar fitowa akan tituna domin yin kira da a sako dukkanin fursunonin siyasa da gidan Sauratar Ali Saud ya bayar da umurnin tsarewa ba.
Tun dai a cikin watan Fabarairun shekarar bara ne mazauna yankin na Qatif da kuma Awamiyya wadanda su ne taskirar dimbin arzikin man fetur da kasar ta mallaka, suka soma gudanar da zanga-zangar lumana domin yin kira da a samar da sauyi a kasar, amma a maimakon sauraren bukatun al'umma, hukumomin kasar sun yanke shawarar ci gaba da yin amfani da karfin wajen murkushe jama'a.
1050187