Bangaren kasa da kasa, shirin zaman lafiya da tsohon sakatare janar na majalisar dinkin duniya kofi Annan ke jagoranta kan kasar Syria na fuskantar manyan matsaloli da za su iya kai shirin nasa ga rugujewa duk kuwa da irin kokarin da ya ce yana yi domin ganin ya zauna ra dukkanin bangarori kan teburin tattaunawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wasu masana na ganin cewa shirin zaman lafiya da tsohon sakatare janar na majalisar dinkin duniya kofi Annan ke jagoranta kan kasar Syria na fuskantar manyan matsaloli da za su iya kai shirin nasa ga rugujewa duk kuwa da irin kokarin da ya ce yana yi domin ganin ya zauna ra dukkanin bangarori kan teburin tattaunawa domin warware matsalar ta hanyar ruwan sanyi.
A nata bangaren gwamnatin Syria ta tabbatar da cewa wani harin ta'addanci da aka kai kasar Siriya ta hanyar tarwatsa wata mota da aka makare da bama bamai ya lashe rayukan mutane akalla 12 tare da jikkata wasu da dama.
Majiyar labaran kasar Siriya ta bayyana cewa: Wata mota da aka cika da bama bamai ta tarwatse a yankin Al-Karamatu da ke garin Homs na kasar Siriya, inda harin ya yi sanadiyyar mutuwan mutane akalla goma sha biyu tare da raunata wasu fiye da goma sha biyar na daban.
Tun a watan Maris na shekarar da ta gabata ce gwamnatin Amurka da 'yan korenta na kasashen Larabawa musamman Qatar, Saudiyya da kuma Turkiyya suke taimakawa 'yan tawayen Siriya, inda daga baya suka fara daukan nauyin tura 'yan ta'adda cikin kasar tare wadata su da makamai domin kifar da gwamnatin Bashar Asad, kuma 'yan ta'addan suna aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula da jami'an tsaro amma kafafen watsa labaran Larabawa da na kasashen Turai suna daura alhakin kisan kan gwamnatin Siriya da nufin tunzura duniya kan daukan matakin soji kan kasar ta Siriya.
1053306