IQNA

Daruruwan Mutane Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Kara Ga Fursunonin Siyasa A Bahrain

17:42 - July 15, 2012
Lambar Labari: 2369085
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zanga-zangar nuna kara ga fursunonin siyasa a kasar Bahrain duk kuwa da irin matakan tsaron da mahukuntan kasar suka dauka na tura sojojinsu da yan sandansu a kan dukaknin manyan tituna domin hana mutane fitowa su bayyana ra’ayinsu kan zalunci da danniya da ake nuna muslu a cikin kasarsu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din alalam cewa, a jiya an gudanar da zanga-zangar nuna kara ga fursunonin siyasa a kasar Bahrain duk kuwa da irin matakan tsaron da mahukuntan kasar suka dauka na tura sojojinsu da yan sandansu a kan dukaknin manyan tituna domin hana mutane fitowa su bayyana ra’ayinsu kan zalunci da danniya da ake nuna muslu a cikin kasarsu duk da tuhumar zalunci da ake musu.
Sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka ta bayyana goyon bayan kasarta ga shirin mai da mulkin kasar Masar ga hannun farar hula karkashin tsarin dimokaradiyya.
A taron manema labarai da ta gudanar da shugaban kasar Masar Muhammad Mursi a yammacin jiya asabar a birnin Alkahira; Hillary Clinton ta furta cewar kasar Amurka tana goyon bayan mika ragamar mulkin kasar Masar ga hannun farar hula karkashin tsarin dimokaradiyya, kuma Amurka tana kaunar ganin ta ci gaba da kasancewa kawar kasar Masar da tafiyarsu zata zo daya.
A yayin ziyarar nata a kasar ta Masar Hillary Clinton ta gudanar da zaman tattaunawa da zababben shugaban kasar Muhammad Mursi, tare da bayyana fatan ganin ya zauna kan kujerar tattaunawa da sojojin kasar don warware takaddamar siyasar da ta kunno kai a kasar.
1052661




captcha