Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren yada labaransa na nahiyar Asia cewa, dubban mutanen birnin Istanbul na kasar Turkiya sun gudanar da wata gagagrumar zanga-zanga a birnin domin nuna rashin amincewarsu da matakan rashin imani da zalunci da mahukuntan kasashen Saudiyya da Bahrain suke dauka kan fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana, daga ciki kuwa hard a aikin ta'addancin da suka yi kan malamin addinin nan na kasar a yankin Awamiyya.
Mutane biyu ne suka rasa rayukansu a cikin gidan yari na Al-Hayer da ke wajen birnin Riyda na kasar Saudiua a lokacinda masu goyon baya da kuma adawa da sarakunan kasar suka yi taho mu gama a cikin gidan yarin, kafin barkewar rikici a cikin gidan yarin, inda sarakunan kasar suke tsare da dubban Fursinonin siyasar kasar, dangin wadanda ake tsare da su a gidan yarin sun yi zanga zanga a ranar jumma'ar da ta gabata inda suka bukatar a saki yanuwansu da tsare a cikin gidan yarin.
Kasar Saudia dai wacce dangin ali -Saud suke mulkinta ta fada cikin rigingimu musamman a yankunan gabacin kasar na Awamiyya da kuma Qadif, inda suke bukatar sauyi a cikin tsarin jagorancin kasar hukumomin kasar ta saudia dai sun dauki matakan tsaro masu tsanani a wadannan yankuna, kuma sun haramta zanga zanga da kuma duk wani abinda zai gurgunta harkokin tsaron kasar.
Al'ummar birnin Istanbul na kasar Turkiya sun gudanar da wata gagagrumar zanga-zanga a birnin domin nuna rashin amincewarsu da matakan rashin imani da zalunci da mahukuntan kasashen Saudiyya da Bahrain suke dauka kan fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana domin neman hakkokinsu da aka haramta musu.
1054754