IQNA

Kungiyar Hadin Kan kasashen Musulmi Ta Yi Kakkausar Suka Kan Cin Zarafin Musulmi A Bama

15:33 - July 17, 2012
Lambar Labari: 2371059
Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi kakkausar suka dangane da cin zarafin mabiya addinin muslunci da mahukuntan kasar Bama suke yi tare da zarginsu da cewa bay an asalin kasar ba ne da nufin kara mayar da su saniyar ware.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC cewa, a jiya kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi kakkausar suka dangane da cin zarafin mabiya addinin muslunci da mahukuntan kasar Bama suke yi tare da zarginsu da cewa bay an asalin kasar ba ne da nufin kara mayar da su saniyar warea cikin dukaknin harkokin kasar.
Bayanin wanda bababn sakataten kungiyar ne ya fitar da shi yay i nuni da cewa, abin da mabiya addinin buda suke na nuna kyama ga musulmi a kasar Bama da kuma yadda mahukuntan kasar suka goyi bayan wannan mataki, hakan yay i hannun riga da koyarwar addinina masu kira zuwa kyawawan dabiu, kamr yadda hakan ya yi hannun riga da dukaknin kidoji da dokoki na kasa da gwamnatin kasar ta ke raya cewa tana bi.
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi kakkausar suka dangane da cin zarafin mabiya addinin muslunci da mahukuntan kasar Bama suke yi tare da zarginsu da cewa bay an asalin kasar ba ne da nufin kara mayar da su saniyar ware bisa zalunci da kama karya, ba tare da wata kasa daga cikin kasashen da raya kare hakkin bil adama ta ce uffan kan wannan lamari ba, kamar yadda gawamnatin wahabiyawan Saudiyya ma ba ta ce komai kan lamarin ba. 1054521
captcha