Kamfanin dillancin labaran iqna ya hgabarta cewa, ya nakalato daga shafin sadarwa na yanar gizo AISP cewa ajiya majalisar mabiya tafarkin iyalan gidan anzon Allah a kasar India ta yi kira da a dakatar da nuna wani fim da aka shirya mai suna Karbala wanda babban kamfanin na sharia fina finan kasar ya shirya da nufin nuna shia cikin azumin mai zuwa tare da bayyana hakan da cewa ya daba wa a bin da aka san kamfanin da yi a cikin lokotan baya.
A makwabciyar kasar ta India kuma wato kasar Pakistan, Mutane 14 ne suka rasa rayukansu a wani harin bom da ya tashi kusa da wata mota a yankin Pishawar arewa maso yammacin kasar Pakistan a yau laraba, labarin ya kara da cewa dukkan mutane 14 da suka rasa rayukansu dangi guda ne kuma sun fito ne daga yankunan da yan shia'a suka fi yawa a kasar ta Pakistan.
Zikir Hussain wani jami'in gwamnati a yankin ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa harin ya auku ne a kauyen Sepoy a dai lokacinda motar da ke dauke da mutanen take wucewa a wani titi a a kauyen.
Husain ya ce da alamun an yi amfani da na'urar sarrafa bom daga nesa ne wajen data bom din.
A cikin wadanda suka rasa rayukansu dai akwai manya manyan mutanen 8 da kuma yara yan shekaru 11 guda biyu, mata biyu da kuma yarinya yar shekara 3 guda daya.
1056878