IQNA

Malaman Makarantar Hauza Ta Imam Khomeini (RA) Sun Ziyarci Bangaren Iqna

13:23 - July 24, 2012
Lambar Labari: 2376382
Bangaren kasa da kasa, wasu daga malaman makarantar hauza ta marigayi Imam Khomeini (RA) da ke kasar Syria sun ziyarci bangaren iqna a taron baje kolin kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Tehran wanda ya fara tun makon da ya gabata kuma zai ci gaba har zuwa karshen watan azumin Ramadan mai alfarma.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na banagren yada labaransa cewa wasu daga malaman makarantar hauza ta marigayi Imam Khomeini (RA) sun ziyarci bangaren iqna a taron baje kolin kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Tehran wanda ya fara tun makon da ya gabata kuma zai ci gaba har zuwa karshen watan azumin Ramadan mai alfarma kamar dai yadad aka saba yia kowace shekara, inda tawagar makarantar daga birnin Damascus take ziyratar taron baje kolin.
A bangare guda kuma tun bayan harin da aka kai kan babban ginin majalisar tsaron kasa a birnin Damascus na kasar Syria a ranar Laraba da ta gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ministan tsaron kasar da mataimakinsa, dakarun gwamnatin kasar ta Syria suka lashi takobin shiga kafar wando daya da 'yan ta'adda da suke kaddamar da irin wadannan hare-hare a cikin kasar, wadanda suke samun goyon baya da taimakon Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila da sauran kasashen turai, gami da 'yan koransu daga cikin gwamnatocin larabawa.
A cikin wani bayani da rundunar sojin Syria ta fitar 'yan sa'oin da suka gabata, ta tabbatar da cewa nan da sa'oi 24 zuwa 48 za a kammala murkushe 'yan ta'adda da suka sadado cikin birnin Damascus suna harbe-harbe, tare da korar mutane daga wasu unguwanni da ke cikin birnin, a daren jiya kawai sojojin gwamnatin Syria sun kashe 'yan ta'adda sama da 150 da suke dauke da makamai a cikin birnin Damascus da wasu yankuna na kasar, yayin da wasu daruruwa suka ajiye makamansu tare da mika wuya bayan da sojojin na Syria suka yi musu kofar raggo.
Rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikin gawawwakin 'yan ta'addan da aka samu wadanda sojin gwamnatin Syria suka harbe bayan musayar wuta mai tsanani a yankin Maidan da Qabun a cikin sa''oi 24 da suka gabata, akwai 'yan kasashe daban-daan da suka hada da Libya, Tunisia, Saudiyya, Kuwait Pakistan Lebanon da sauransu, lamarin da ya sanya da dama daga cikin masu bin diddigin lamuran da ke faruwa a Syria suke ganin cewa, abin da ke faruwa a kasar dadadden shiri ne da aka shirya daga wajen kasar, da ba shi da wata dangantaka da boren kasashen larabawa, domin kuwa Amurka da sauran kasashen turai da yan koransu daga cikin kasashen larabawa su ne suke jagorantar rikicin da ke faruwa a Syria, su ne suke aikewa da mayaka da makamai da kudade, wani ban mamaki kuma a nan shi ne, daga cikin mayakan da Amurka da sauran kasashen larabawa suke aikewa zuwa Syria har da 'yan alkaida, wadanda Amurka da turawa suka ce suna yaki da su a Iraki da kuma Afghanistan da Pakistan.
1060850


captcha