IQNA

Wasu Daga Cikin Malamn Yahudawan Sahyuniya Sun Kai Farmaki A kan Masallacin Qods

15:22 - July 24, 2012
Lambar Labari: 2376544
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin malaman yahudawan sahyuniya sun kai samame kan masallacin Qods mai alfarma da nufin muzgunawa al’ummar palastinu marassa kariya da suke gudanar da ayyukansu na ibada a wurin tsawon shekaru kasantuwar wurin mallakinsu ne.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a cikin makon nan wasu daga cikin malaman yahudawan sahyuniya sun kai samame kan masallacin Qods mai alfarma da nufin muzgunawa al’ummar palastinu marassa kariya da suke gudanar da ayyukansu na ibada a wurin tsawon shekaru kasantuwar wurin mallakinsu ne, wanda kuma yahudawan suke ikirarin cewa nasu ne tun kaka da kakanni.
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Siriya na nuni da cewa hankula sun fara kwantawa a babban birnin kasar Damaskus bayan da sojojin kasar suka sami nasarar fatattakar dakarun 'yan ta'addan kasar daga mafi yawa daga yankunan da suka kama su a baya a birnin Damaskus din da kewayensa.
Rahotannin sun ce dakarun kasar Siriyan sun sami nasarar kwace yankin haramin Sayyida daga hannun 'yan ta'addan kamar yadda kuma suka sami nasarar kama wasu daga cikin 'yan ta'addan da suke kokarin kai harin kunar bakin wake cikin haramin. Har ila yau rahotannin sun ce dakarun kasar Siriyan sun sami nasarar fatattakan masu dauke da makamin daga yankunan Dariya da Harsta inda suka sami nasarar kashe na kashewa da kuma kama na kamawa, wasu kuma daga cikinsu sun mika kansu.
Wasu rahotannin suna nuni da cewa har ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da barin wuta tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen a wasu yankuna na kasar Siriya, kamar yadda kuma dakarun Siriyan sun sami nasarar sake kwato kan iyakokin kasar da 'yan ta'addan suka kwace in banda waje guda dake tsakanin iyakar kasar da kasar Turkiyya inda ake ce daruruwan masu dauke da makami 'yan sauran kasashen larabawa suna ci gaba da rike shi.
Kasashen Saudiyya da Qatar da Turkiyya dai suna daga cikin kasashen da suke ba wa 'yan ta'addan makamai da sauran kayayyakin aikin da suke bukata da nufin kifar da gwamnatin kasar mai tsananin adawa da yahudawa da kasashen yammacin turai.
1060639
captcha