Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa cewa, a birnin Tehran bisa la’akari da mawuyacin halin da al’ummar kasar Myanmar suke ciki wannan ya sanya an fara tara kudade na taimako ga al’ummar wannan kasa domin taimaka musu da abin da suke bukata na daga abinci da sauransu da kuma kayayakin sakawa inda mutane ke ci gaba da bayar da taimakonsu ga yan uwansu musulmi.
Wasu masu bin diddigin lamurran da suke faruwa na siyasar kasashen larabawa sun imanin cewa, Muhammad Mursi yana da babban kalu bale a gabansa, kasantuwar cewa da dama daga cikin mutanen da suka jefa masa kuri'a suna da fatan ganin ya yanke alakar kasar Masar da haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da taimaka ma al'ummar palastinu, sabanin gwamnatin Husni Mubarak da ta kasance babbar kawa ga Isra'ila, da ake hada baki da ita wajen cutar da al'ummar palastinawa.
Bugu da kari kan hakan, wasu daga cikin kasashen larabawa da suke dasawa da Amurka kuma suke kare manufofinta a cikin kasashen larabawa da na musulmi a halin yanzu kamar Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa, ba su lale marhabin da zabar Mursi a matsayin shugaban kasar Masar ba, domin kuwa sun yi iyakacin kokarinsu wajen kasha biliyoyin kudade domin muguda sakamakon zaben na kasar Masar da nufin kayar da Mursi amma hakan bai kai ga nasara ba, wannan ne ma ya sanya Mursi yake kokarin tabbatarwa irin wadannan kasashen larabawa da cewa ba zai mayar da hankali kan abubuwan da suka faru ba, maimakon haka yana neman hadin kansu domin tunkarar gaba.
Yanzu dai za a iya cewa kasashen Amurka da sauran kawayenta larabawa musamman Saudiyya, suna baiwa Mursi rata ne domin su ga kamun luddayinsa, idan har zai iya tafiya da salon siyasa da zai kare manufofinsu, ko da kuwa bai kai kamar yadda babban aminsu Husni Mubarak ya kasance yanayi ba, to za su iya daga masa kafa, a matsayin rashin uwa a kan yi uwa daki kamar dai yadda hakan shi ne salon siyasar munafunci.
1060374