IQNA

Saudiyya Na Da Mummunar Manufa Ta Boye Kan Kiran Zaman Taron Kasashen Musulmi

14:35 - July 25, 2012
Lambar Labari: 2377444
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Saudiyya tana da boyayyar manufa ta kiran taron gaggawa na kasashen musulmi inda ga dukakn alamu tana son cimma wata manufa ta siyasa a boe da ko shakka babu za ta amfanar da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila da hakan wanda kuma tuni al’ummomin musulmi suka fara gano hakan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa da dama daga cikin masana sun yi imanin cewa gwamnatin Saudiyya tana da boyayyar manufa ta kiran taron gaggawa na kasashen musulmi inda ga dukakn alamu tana son cimma wata manufa ta siyasa a boe da ko shakka babu za ta amfanar da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila da hakan wanda kuma tuni al’ummomin musulmi suka fara gano hakan kamar yadda ba sabon lamari ba ne a gare ta.
Kasar Iran ba zata canza matsayinta ba tare da duk irin takura mata da kasashen yamma suke yi. Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee ne ya bayyana haka a jiya talata a lokacin da yake ganawa da jami'an gwamnatin kasar a gidansa a nan Tehran.
Jagoran ya kara da cewa, takunkumin tattalin arziki wanda kasashen yamma tare da jagorancin kasar Amurka suka dorawa kasar ba zai taba durkusadda gwamnatin kasar Iran zuwa ga bukatun wadannan kasashe ba.

Sun fake da shirin nuclear kasar Iran da kuma kare hakkin bil'adama a kasar, amma babbar manufarsu ita ce ganin bayan tsarin Musulunci wanda yake jagorancin kasar tun fiye da shekaru 30 da suka gabata, tsarin da ya ce yana samun goyon bayan alummar kasar.
Muna ganin irin matsalolin da suma wadannan kasashen suke fama da su, da kuma irin koma bayan da musamman kasar Amurka suka fuskanta a kasashen Afganistan Iraqi da kuma sauran kasashen duniya.

Jagoran ya kara da cewa, matsalolin tattalin arzikin da kasahen turai da kuma Amurkan kanta suka fuskanta a halin yanzu yana dada nuna mana cewa nasara tana gaba.

1061429


Gwamnatin Kasar Kenya Ware wasu Kudade Domin Taimaka Ma Makarantun Kur’ani

Bangaren siyasa, gwamnatin kasar Kenya ta ware wasu kudade domin taimaka ma makarantun kur’ani da suke gudanar da harkoki na ilimin littafi mai tsarki tare da koyar da talibai karatunsa da kuma sanin kaidojin karatunsa kamar dai yadda sakataren ma’aikatar ilimi ta kasar ya sanar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labarai cewa, gwamnatin kasar Kenya ta ware wasu kudade domin taimaka ma makarantun kur’ani da suke gudanar da harkoki na ilimin littafi mai tsarki tare da koyar da talibai karatunsa da kuma sanin kaidojin karatunsa kamar dai yadda sakataren ma’aikatar ilimi ta kasar ya sanar da manema labarai.

A wani labarin na daban kuma mutanen kasar Ivory Coast yan gudun hijira wadanad aka kaiwa hari a sansaninsu da ke garin Dueku a daren jumma'a da ta gabata sun dorawa jami'an tsaron MDD wadanda suke gadin sansanin da laifin rashin karesu daga maharani, a daren jumma'an da ta gabat ce wasu mutanen dauke da kulake da kuma adduna su kimani 300 ne suka fadawa sansanin yan gudun hijirar wadanda suka kauracewa gidajensu sanadiyyar rikicin bayan zaben shugaban kasa na shekara ta 2010, suka kashe mutane 7 daga cikinsu sannan suka raunata wasu hamsin.

Wani dan gudun hijira wanda ya sami raunuka a harin na daren jumma'a mai suna Sidiki Kehi ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa a lokacin da maharan suka zo, sun balle kofar shihga sansanin, suka fara keta tentunan da yan gudun hijira kimani suke cikinsa suna ta kona su, sidiki Kehi ya ce, ya guda ya je wajen jami'an tsaron wadanda suke gadin wurin, ya hau motarsu amma sai suke bankado shi ya fadi a kasa, inda maharani suka yi masa dukan kawo wuka, Allah ne kawai ya yi zai tsira da ransa inji shi.

Majalisar dinkin duniya ta samar da jami'an tsaro na UNOCI ne don kare wadan nan yan gudun hijira, amma sun kasa yin haka. Jami'an majalisar dinkin duniya dai sun ce ba zasu ce kome kan lamarin ba har sai sun kare bincike.

1061402





An Bude Wani Taron Baje Koli Na Rubutun Musulunci A Birnin Lahour

Bangaren kasa da kasa, an bude wani taron baje koli na kyakyawan rubutun Musulunci a birnin Lahour na kasar Pakistan tare da halartar wakilan cibiyoyin addini da kuma madaba’antu na kasar da suke gudanar da ayyuka na buga littafai da kuma rubuce-rubucen addini.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Times, cewa an bude wani taron baje koli na kyakyawan rubutun Musulunci a birnin Lahour na kasar Pakistan tare da halartar wakilan cibiyoyin addini da kuma madaba’antu na kasar da suke gudanar da ayyuka na buga littafai da kuma rubuce-rubucen addini da nufin kara fitoda matsayin addini da kuma gudunmawar da yake bayarwa a bangaren aladu da fasaha.

Wani rahoton kuma ya habarta cewa jJirgin sama maras matuki da Amurka ke amfani da shi domin kashe fararen hula, a safiyar yau ya kashe mutane akalla 10 a cikin yankunan kabilu da ke kusa da iyakar Afghanistan da kuma Pakkistan bisa zargin cewa wai su 'yan ta'adda ne.

Rahotanni sun ce jirgin ya harba makamai masu linzame akalla 6 a kan gidajen jama'a da ke kauyen Dray Nashtar na lardin Miranshah da ke cikin kasar Pakistan, inda kuma kamar yadda ta saba, hukumar leken asiri ta amurka wacce ke amfani da wadannan jirage ta ce wadanda ta kashen dukkaninsu 'yan ta'adda ne, alhali kuwa mazauna kauyen sun ce mutanen ba su da wata alaka da ayyukan tsageranci.

A can baya dai alkalumma sun yi nuni da cewa dubban mutane da ke rasa rayukansu sakamakon wadannan hare-hare na jiragen maras matuka, fararen hula ne amma ba 'yan ta'adda ba kamar yadda Amurkar ke ikirari.

1061301











Taron Buda Baki Da Ya Hada Musulmi Da Kirista A Garin kaduna Da ke Nigeria

Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taron buda baki wanda ya hada mabiya addinin muslunci da suka yi azumi da kuma mabiya addinin kirista domin kara dankon alaka da zumunci tsakanin bangarorin biyu da suka kwashe tsawon shekaru suna rayuwa tare da juna duk kuwa da matsalolin da ake ta kokarin haddasawa a tsakaninsu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam, cewa an gudanar da wani taron buda baki wanda ya hada mabiya addinin muslunci da suka yi azumi da kuma mabiya addinin kirista domin kara dankon alaka da zumunci tsakanin bangarorin biyu da suka kwashe tsawon shekaru suna rayuwa tare da juna duk kuwa da matsalolin da ake ta kokarin haddasawa a tsakaninsu wanda kai tsaye ake zargin cewa kasashen ketare da suke tare da yahudawan sahyuniya suna da hannu a ciki.

A wani bangare kuma na siyasar kasar komitin bincike na shugaban tarayyar Nigeria kan almundahanar kudaden tallafin man fetur a kasar ya bayyana cewa kamfanonin yan kasuwa wadanda suke shigo da man fetur daga kasashen waje sun karbi naira biliyon 382 daga asusun gwamnati ba tare da sun shigo da ko digo guda na man fetur ba.
Komitin binciken dai karkashin jagorancin Imokhuede, yana daga cikin jeren komiti komiti wadanda suka gudanar da bincike kan wannan almundahanar, kuma ya tabbatar da cewa jami'an gwamnati da dama suna da hannu a cikinsa, Imokhuede, ya bayyana haka ne a jiya a lokacin da yake mikawa shugaba Good luck Jonathan sakamakon binciken komitin nasa.
Shugaban komitin bai ambaci sunan wani kamfani ba, amma ya ce mataki na gaba shi ne shirin gabatar da wadannan kamfanoni da jami'an gwamnatin da suke da hannu cikin almundahanar da kuma auditoci masu zaman kansu wadanda suka kula da shirin bada kongilar a gaban kotu.
1061260









captcha