IQNA

Yahudawan Sahyuniya Suna Keta Alfarmar Masallacin Qods Mai Alfarma

14:00 - July 26, 2012
Lambar Labari: 2377898
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya suna ci gaba da keta alfarmar masallacin Qods mai alfarma a wani mataki na tozarta dukaknin wurare da suke da tsarki ga musulmi a cikin yankunan palastinawa da suke mamye da su kamar dai yadda rahotanni suka tabbatar.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Rahotannin da suke fitowa daga kasar Siriya na nuni da cewa sojojin kasar na ci gaba da fatattakan 'yan tawaye masu dauke da makami da suka yi tunga a wasu yankuna da ke wajen babban birnin kasar, kamar yadda kuma suke ci gaba da kai hare-hare kan tungar masu dauke da makamin a garin Halab.

Majiyoyin sojin kasar Siriyan sun ce dakarun sojin sun nufi garin Halab inda 'yan ta'addan da suke samun makamai daga kasashen Saudiyya da Qatar da Turkiyya suka yi tunga a can da nufin fatattakansu. Rahotannin sun ce sojojin Siriyan sun sami nasarar fatattakan masu dauke da makamin a wasu yankuna na garin bayan sun kashe wasu daga cikinsu da kuma kame wasu.

A bangare guda kuma ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya zargi kasar Amurka ta kwadaitar da ayyukan ta'addanci a kasar Siriya sakamakon kin yin Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai cibiyar tsaron kasar Siriyan da ya yi sanadiyyar mutuwan manyan jami'an tsaron kasar ciki kuwa har da ministan tsaro da mataimakinsa.

Har ila yau minista Lavrov ya yi watsi da bukatar ziyarar kasar da ministan harkokin wajen Qatar da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa suka gabatar yana mai cewa babu bukatar su zo din idan har za su zo maganar saukar shugaban kasar Siriya Bashar al-Asad ne kamar yadda suka gabatar a baya.

1062163


captcha