IQNA

Iran Da Kuma Gwagwarmaya Na Fuskantar Yakin Ruwan Sanyi A yau

19:35 - July 27, 2012
Lambar Labari: 2378435
Bangaren kasa da kasa, jamhuriyar muslunci ta Iran da kuma gwaggwarmayar neman yanci a yanki suna fuskantar gagarumin yaki na kwakalwa da kuma yakin ruwan sanyi ta hanyoyi da dama da nufin kawo karshen duk wani abin da zai iya girgiza samuwar haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin.
Kmafanin dilalncin labran iqna ya habarta cewa, yanakalto daga shafin sadarwa cewa, masana da dama a yankin gabas ta tsakiya sun yi imanin cewa jamhuriyar muslunci ta Iran da kuma gwaggwarmayar neman yanci a yanki suna fuskantar gagarumin yaki na kwakalwa da kuma yakin ruwan sanyi ta hanyoyi da dama da nufin kawo karshen duk wani abin da zai iya girgiza samuwar haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin na gabas ta tsakiya.
Shi kuwa kamfanin dillancin labaran Tarand na kasar Azarbaijan ya fi ba da muhimmanci ne da bangaren da Jagoran ya yi bayanin irin nasarorin da juyin juya halin Musulunci ya kawo wa kasar Iran yana mai cewa juyin juya halin ya kawo wa al'ummar Iran 'yanci maimakon mulkin kama-karya na tsohuwar gwamnatin kasar kamar yadda kuma ya kifar da gwamnatin da take adawa da Musulunci da kuma maye gurbinta da gwamnati irin ta Musulunci mai girmama ra'ayin al'umma.
Ita kuwa jaridar Yediot Aharanot ta HKI ta zabi bangaren da Jagoran ya bayyanar HKI a matsayin cutar kansa ce a matsayin babban kanun labaranta, sannan kuma a cikin sharhinta ta fi ba da muhimmanci ne ga bangaren da Jagoran yace duk wani kokarin da Amurka ta yi wajen kara kakabawa Iran takunkumi da kuma yi mata barazana hakan zai fi cutar da Amurkan ne kafin ya cutar da Iran. Shi kuma kamfanin dillancin labaran kasar Jamus cewa ya yi daga maganganun da Jagoran ya yi ana iya fahimtar cewa Iran ba za ta taba ja da baya daga wannan shiri nata na nukiliya wai saboda barazanar takunkumi ko harin soji ba. Har ila yau kuma wani bangaren da kamfanin dillancin labaran ya fi ba shi muhimmanci shi ne bangaren da jagoran ya yi ishara da cewa Amurka tana tsoron tattaunawa da Iran ne saboda ba ta da wata hujja da ta yi daidai da hankali.
1062999

captcha