IQNA

An Nuna Wani Littafi Mai Suna Ahlul Bait (AS) A Cikin Kur’ani A Taron Baje Koli

12:10 - July 28, 2012
Lambar Labari: 2378893
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani littafi mai suna iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka a babban taron baje kolin kur’ani na duniya da ke gudana a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a cikin gida, cewa , an nuna wani littafi mai suna iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka a babban taron baje kolin kur’ani na duniya da ke gudana a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran.
A wani labarin na daban kuma kasar Iran ba zata canza matsayinta ba tare da duk irin takura mata da kasashen yamma suke yi. Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee ne ya bayyana haka a jiya talata a lokacin da yake ganawa da jami'an gwamnatin kasar a gidansa a nan Tehran, jagoran ya kara da cewa, takunkumin tattalin arziki wanda kasashen yamma tare da jagorancin kasar Amurka suka dorawa kasar ba zai taba durkusadda gwamnatin kasar Iran zuwa ga bukatun wadannan kasashe ba.

Sun fake da shirin nuclear kasar Iran da kuma kare hakkin bil'adama a kasar, amma babbar manufarsu ita ce ganin bayan tsarin Musulunci wanda yake jagorancin kasar tun fiye da shekaru 30 da suka gabata, tsarin da ya ce yana samun goyon bayan alummar kasar, muna ganin irin matsalolin da suma wadannan kasashen suke fama da su, da kuma irin koma bayan da musamman kasar Amurka suka fuskanta a kasashen Afganistan Iraqi da kuma sauran kasashen duniya.

Jagoran ya kara da cewa, matsalolin tattalin arzikin da kasahen turai da kuma Amurkan kanta suka fuskanta a halin yanzu yana dada nuna mana cewa nasara tana gaba.

1063542




captcha