IQNA

Makiya Na Kokarin Ganin Rikicin Syria Ya Kara Muni Domin Cimma Manufofinsu Na Siyasa

12:10 - July 28, 2012
Lambar Labari: 2378896
Bangaren kasa da kasa, shugaban kwamitin gwagwarmayar kwato yankin palastinu daga hannun yahudawan sahyuniya yan mamaya ya bayyana cewa babbar manufar makiyan al’umma kan rikicin Syria it ace rusa kasar ta yadda hakan zai bas u damar cimma manufofinsu na siyasa a kan gwamnati.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cew ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa shugaban kwamitin gwagwarmayar kwato yankin palastinu daga hannun yahudawan sahyuniya yan mamaya ya bayyana cewa babbar manufar makiyan al’umma kan rikicin Syria it ace rusa kasar ta yadda hakan zai bas u damar cimma manufofinsu na siyasa a kan gwamnatin kasar wadda bas u dasawa da ita a tarihi.
Ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewar gwamnatin Siriya da sojojin kasar suna da karfin murkushe 'yan ta'adda da kansu, a ganawar da ya yi da manema labarai a yau laraba; ministan tsaron kasar Iran Brigadier Janar Ahmad Wahidi ya bayyana cewar gwamnatin Siriya da sojojin kasar suna da karfin kalubalantar duk wani aikin ta'addanci da kansu, kuma a halin yanzu haka suna samun gagarumar nasara a kokarin da suke yi na murkushe 'yan ta'adda a sassa daban daban na kasar.
Wannan furuci na Janar Wahidi ya zo ne a matsayin mai da martaki kan zargin cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana taimakawa kasar Siriya ta hanyar karfin soji, har ila yau ministan tsaron kasar ta Iran ya kara da cewar manyan kasashe masu girman kai a duniya suna tattaro kan 'yan ta'adda daga kowane sako na duniya tare da aikewa da su zuwa kasar Siriya, amma suna kokarin kawar da hankula duniya daga kan wannan danye aiki na su ta hanyar zargin kasar Iran da taimakawa kasar Siriya da karfin soji.
1063627




captcha