Bangaren kasa da kasa, a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Masar a jiya a birnin Alkahira Isma’il Haniyya ya bayyana cewa al’ummar na da matukar bukatuwa zuwa taimakon shugaba Mursi musamman kan batun wutar lantarki da janye takunkumin da masar ta kaka ba musu tun tsawon shekaru.
Kmafanin dilalncin labaran qna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Masar a jiya a birnin Alkahira Isma’il Haniyya ya bayyana cewa al’ummar na da matukar bukatuwa zuwa taimakon shugaba Mursi musamman kan batun wutar lantarki da janye takunkumin da masar ta kaka ba musu tun tsawon shekaru da suka gabata a karashin shugabancin fir’ananci na Husni Mubarak.
A wani labarin na daban kuma shugaban kasar Masar Muhammad Mursi zai kawo ziyarar aiki a nan kasar Iran a watan Agusta domin halartar taron koli na kungiyar Yan Ba Ruwanmu wanda za a gudanar a birnin Tehran hakazalika zai tattauna batutuwa da su ka shafi kasashen biyu, tare da jamian gwmantain kasar Iran.Jaridar Al-Safir ta kasar Labanan ce ta kawo wannan labari tare da kuma cewa ana tsammanin za a sami kyautatuwar alaka tsakanin Iran da Masar a yan makonni masu zuwa.
Tun bayan faduwar gwamnatin Husni Mubarak na kasar Masar jamian gwamanatin Iran da na Masar suke ta bayyana shawaarsu ta maida cikakken huldar jakadanci tsakanin kasashen nasu.Minsitan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salehi ya gana da tsohon tawaran aikinsa na kasar Masar Nabil al-Arabi a gefen zauren taron kungiyar Yan Ba Ruwanmu da aka yi a garin Bali na kasar Indonisiya, inda kuma suka yi musayar raayi kan hanyoyin karfafa alakoki tsakanin Tehran da Alkahira.
1063301