Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewaya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Rafidin, cewa limamamn masattai a garuruwan Najaf da Karbala da ke kudancin kasar Iraki sun yi kakakusar suka da yin Allawadai da kisan kyashin da ake yi wa musulmin kasar Myanmar saboda zalunci da danniya da rashin tausayi balanta kare hakkokinsu a matsayinsu nay an ksa bisa hujjar cewa daruruwan shekaru da suka gababta ne kakaknninsu suka zo kasar.
Dangane da sha'anin na Iraki kuwa priministan kasar ya zargi masu iko a yankin Qurdawa wadanda mai kwaya kwaryan cin gashin kai da sabawa dokokin kasar ta Iraqi a lokacinda suka hana sojojin kasar isa kan iyakokin kasar da kasar Syria da ke yankin na Qurdawa.
A ranar laraba da ta gabata ce jami’an tsaron yankin Qurdawan, suka hana sojojin kasar Iraqi isa zuwa yankin kan iyaka da ke Zummer don tabbatar da cewa rikicin da ke faruwa a kasar Syria bai shigo kasar ba.
Maliki ya yi gargadin cewa idan wannan halin da qurdawa suke nuna ya ci gaba zai iya haddasa rigima tsakaninsu da jami’an tsaron kasar ta Iraqi, wakilan qurdawa a majalisar dokokin kasar Iraqi dai sun bayyana cewa gwamnatin tarayyar kasar bata tuntubi hukumomin yankin Qurdawan ba kafin ta aike da sojojinta zuwa yankin.
Kasar Syria dai tana fama da tashe tashen hankula tun watan maris na shekara ta 2011, kuma tuni rikicin kasar ta shafi wasu kasashen da suke makobtaka da ita kamar Lebanon da kuma Turkiyya.
1063812