Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin mutanen kasar Masar sun gudanar da wani gangami suna neman bayar da kariya ga masalalcin Qods da a halin yanzu yake fuskantar barazana daga yahudawan sahyuniya masu tsaurin ra’ayi tare da tabbatar da cewa an kawo karshen barazanarsu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI cewa wasu daga cikin mutanen kasar Masar sun gudanar da wani gangami suna neman bayar da kariya ga masalalcin Qods da a halin yanzu yake fuskantar barazana daga yahudawan sahyuniya masu tsaurin ra’ayi tare da tabbatar da cewa an kawo karshen barazanarsu kan wannan masallaci mai alfarma.
A nasa bangaren shugaban kasar Masar Muhammad Mursi zai kawo ziyarar aiki a nan kasar Iran a watan Agusta domin halartar taron koli na kungiyar Yan Ba Ruwanmu wanda za a gudanar a birnin Tehran hakazalika zai tattauna batutuwa da su ka shafi kasashen biyu, tare da jamian gwmantain kasar Iran.Jaridar Al-Safir ta kasar Labanan ce ta kawo wannan labari tare da kuma cewa ana tsammanin za a sami kyautatuwar alaka tsakanin Iran da Masar a yan makonni masu zuwa.
Tun bayan faduwar gwamnatin Husni Mubarak na kasar Masar jamian gwamanatin Iran da na Masar suke ta bayyana shawaarsu ta maida cikakken huldar jakadanci tsakanin kasashen nasu.Minsitan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salehi ya gana da tsohon tawaran aikinsa na kasar Masar Nabil al-Arabi a gefen zauren taron kungiyar Yan Ba Ruwanmu da aka yi a garin Bali na kasar Indonisiya, inda kuma suka yi musayar raayi kan hanyoyin karfafa alakoki tsakanin Tehran da Alkahira, wanda hakan yana daya daga cikin abin da masana suke kallonsa a matsayin wani lamari da zai karfafa muslunci da Kalmar musulmi a duniya.
1064659