IQNA

Isar Da Sakon Musulunci Aiki Ne Da Ya Rataya Kan Dukkanin Musulmi

17:48 - July 29, 2012
Lambar Labari: 2380177
Bnagaren kasa da kasa, isar da sakon addinin mulunci aiki ne da ya rataya a kan dukaknin muuslmi baki daya domin babu wani wanda yay i imani da Allah face ya rataya kansa ya isar da sakon ubangiji ga sauran al’ummomi ta hanyar da ya samu damar yin hakan ko da kuwa ta hanyar nuna kyakyawan dabiu ne kawai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na gulftoday, cewa isar da sakon addinin mulunci aiki ne da ya rataya a kan dukaknin muuslmi baki daya domin babu wani wanda yay i imani da Allah face ya rataya kansa ya isar da sakon ubangiji ga sauran al’ummomi ta hanyar da ya samu damar yin hakan ko da kuwa ta hanyar nuna kyakyawan dabiu ne kawai domin hakan shi ne gishin yin nasara wajen isar da sakon muslunci.
Dangane da kisan da ake yi wa musulmi kuwa a Myanmar Kawo ya zuwa yanzu lamirin duniya bai girgiza ba akan kisan da ake yi wa musulmin mayyamar da kona gidajensu da shagunansu na kasuwanci. Babu wanda ya zubar da koda hawaye akan musulmi dubu dari takwas da rayuwarsu ta ke fuskantar bakar wahala. Shin saboda mutanen da ake kashewa a muyammar musulmi ne, ko kuma saboda tsiraru ne? Yadda al'amurra su ke tafiya a cikin kasar ta Muyammar a yanzu na nuni da cewa za a ci gaba da samun asarar rayuka anan gaba, tunda dai babu alamar za a takawa masu makasa birki. Ga dukkanin alamu'kisan da 'yan budda su ke yi wa musulmi a cikin Muyammar suna yi ne da tallafin gwamnatin kasar. Su ke kuma korarsu daga gidajensu da maida su zama 'yan gudun hijira na tilas.
A tsammani shi ne addinin Budda wanda ya yi imani da halin kirki da kyautatawa halittu, da s u ke kira Neravana, su zama masu kyautatawa abokan zama da su. A lokacin da 'yan taliban su ka tarwatsa gumakan Budda a Afgahnistan , wadannan musulmin da ake kashe wa a yanzu sun yi Allah wadai da Taliban su ka kuma bayyana abinda su ka yi da cewa keta ce da mugunta. Daruruwan shekaru musulmin kasar Thalidan su ka yi suna rayuwa da mabiya addinin Budda, amma ana samun sauyin siyaya a cikin kasar sai abokan zamansu su ka ci amanarsu da fara kashe su.
Da gangan ake son nuna cewa a duk inda musulmi su ke a duniya masu son tada hankali ne. Wannan siyasa ce yammacin turai ke amfani da ita a lokaci mai tsawo. Wannan kuwa ba shi ne karon farko ba da aka yi wa musulmin mayammar kisan kiyashi. A tsawon lokacin mulkin sojan wannan kasa sun zama zakaran gwajin dafi na nuna kiyayya a gare su.
Abin da ake sa ran kungiyoyin kasa da kasa su aikata shi ne kawo karshen wannan irin kisan da ake yi wa musulmin muyammar, saboda su ma su rayu daidai da kowace al'umma a duniya. Idan a tsawon shekarun baya har zuwa 2010 gwamnarin Mayammar ta kasance a cikin killcewa daga kasashen duniya saboda mulkin soja na kama-karya, to shakka babu kisan kiyashin da ta ke yi wa musulmi zai maida ita zama mai laifi akalla a idon sauran musulmin duniya. 1064178






captcha