IQNA

Wasu Alamu Sun Nuna Cewa Fadakar Musulmi Ta Razana Mahukuntan Habasha

12:50 - July 30, 2012
Lambar Labari: 2380853
Bnagaren kasa da kasa, wani mai sharki kan lamurran da suke kai da komowa ya bayyana cewa irin matakan da mahukuntan kasa Habasha suka fara dauka a cikin yanlokutannan na takura mabiya addinin mulucni hakan wata alama ce da ke tabbatar da cewa fadakar musulmia duniya ta razana su.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam, cewa wani mai sharki kan lamurran da suke kai da komowa ya bayyana cewa irin matakan da mahukuntan kasa Habasha suka fara dauka a cikin yanlokutannan na takura mabiya addinin mulucni hakan wata alama ce da ke tabbatar da cewa fadakar musulmi a duniya ta razana su mahukuntan na kasar Habasha, duk kuwa da cewa musulmi su ne marassa rinjaye a kasar.
A ranar Litinin da ta gabata ne aka kammala taron kasa da kasa kan Matasa da Farkawar Musulmi wanda aka gudanar a birnin Tehran. A wannan zama na kwanaki biyu, matasa kimani dubu daya masu gudanar da ayyukan fafutuka a fagage daban daban na siyasa, aladu, da aikin jarida daga kasashe 73 da ita kanta kasar Iran mai masaukin baki ne suka halarta. A bikin rufe taron, babban magatakardan Cibiyar Farkawar Musulmi ta Kasa da Kasa Dakta Ali Akbar Velayati ya bayyana cewa wannan taron matasa da farkawar na farko mafari ne mai albarka wanda sannu a hankali za'a ga tasirinsa a kan matakan da za'a dauka nan gaba wadanda kuma zasu taimaka wajen farfadowar alummomin Musulmi.
Dakta Velayati ya kara da cewa manufar gudanar da wannan taro shi ne samar da yanayi da ya dace domin tattaunawa da musayar ra'ayi tsakanin matasan Musulmi na kasashe daban daban na duniya. A karshen wannan taron an fitar da takardar bayan taro mai bayanai 17 wadanda suka jaddada muhimman batutuwa, ga kuma uku daga cikinsu kuma su ne: farkawar kasashen Musulmi ta sami asali ne daga koyarwar addinin Musulunci; wannan farkawa zata taimaka wajen hada kan Musulmi wanda kuma zai baiwa alummomin Musulmi alkibla da ci gaba a rayuwarsu; aiki bisa tunani da hankali da kuma kiyaye adalci a matsayin hanyar cin nasara.Wannan batu na uku da muka ambata, wato yin aiki na hankali da adalci shi ne muhimmin dalilin da ya taimaka wa masu juyi wajen samun gagarumar nasara a baya bayan a kasashe kamar Tunisiya da Masar.
A fili yake cewa tsattsaurar raayi yana kawo rarraba a cikin alumma, da bata fuskar Musulunci ta hakika, da kuma ba da dama ga kasashe majiya karfi masu kuma adawa da Musulunci su yi katsalanda a kasashen Musulmi. Wani muhimmin abu kuma shi ne rawar da matasa suka taka a farkawar alummomin Musulmi a tsawon shekara daya da ta gabata, kuma wannan guguwa ta girgiza masu iko kama daga arewacin Afirka har zuwa kasashen yankin Tekun Pasha.Wannnan guguwa ta kawar da shugabanni yan kama karya wadanda kuma iyayen gidansu Turawa suke kira masu daidaiton siyasa, wato Zainulabidin bin Ali na Tunisiya, Husni Mubarak na Masar da Ali Abdallah Saleh na Yaman, wadanda kuma yan koren kasashen Yamma ne. 1064297
captcha