IQNA

Wasu Na Kokarin Kone Kur’ani A Libya Bisa Hujjar Cewa Akwai Sa Hannun Gaddafi A Ciki

15:29 - July 30, 2012
Lambar Labari: 2381076
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin masu tsatsauran ra’ayi a kasar Libya sun kudiri aniyar kone wasu kwafin kur’ani mai tsarki bisa hujjar cewa akwai sa hannun tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar marigayi kanar Gaddafi lamarin da ya harzuka al’ummar musulmi na kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Dunya Alwatan cewa, wasu daga cikin masu tsatsauran ra’ayi a kasar Libya sun kudiri aniyar kone wasu kwafin kur’ani mai tsarki bisa hujjar cewa akwai sa hannun tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar marigayi kanar Gaddafi lamarin da ya harzuka al’ummar musulmi na kasar ta Libya da ke fama da matsaloli.
Ton bayan kisan gillar da yan tawayen na kasar ta Libya suka yi ma tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a cikin watan Agustan shekarar da ta gabata, har inda yau take kasar ba ta samu zaman lafiya ba, domin kuwa suna cikin tashin hankali da rashin natsuwa, kamar yadda makamai suka yawaiyta ahannun jama’a kuma ana yin kisan gilla kan mutane.
Labarin ya tabbatar da cewa wasu daga cikin masu tsatsauran ra’ayi a kasar Libya sun kudiri aniyar kone wasu kwafin kur’ani mai tsarki bisa hujjar cewa akwai sa hannun tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar marigayi kanar Gaddafi lamarin da ya harzuka al’ummar musulmi na kasar, wadda ta fuskanci tashin hankali a shekarar da ta gabata.
1065293

captcha