Bangaren kasa da kasa, dubban mutane masu kishin islama a kasar Jordan kakkausar suka da yin Allawadai da matakan da yahudawan sahyuniya suke dauka na wuce gonad a iri wajen kisan gilla kan fararen hula palastiwa a birnin Qods da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da suke cikin wannan babban birnin mai tsohon tarihi.
Kamfanin dilalncn labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Info, cewa a yammacin jiya dubban mutane masu kishin islama a kasar Jordan kakkausar suka da yin Allawadai da matakan da yahudawan sahyuniya suke dauka na wuce gonad a iri wajen kisan gilla kan fararen hula palastiwa a birnin Qods da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da suke cikin wannan babban birnin mai tsohon tarihi kamar yadda Allah ya bayyana shi da cewa ya albarci gefensa.
Kamar dai yadda kowa ya sani wannan dai bas hi ne karon farko da sojojin yahudawan ahyuniya suke hana palastinawa shiga masallacin ba domin gudanar da harkokinsu an ibada, domin kuwa tun amakon day a gabata an hana su shiga domin su yi salla, kuma hakan bay a rasa nasaba da gabatowar lokacin gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga masallacin mai alfarma da marigayi Imam Khomeini ya asssa tun tsawon shekaru kusan talatin.
Bayanin ya tabbatar da cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana daruruwan palastinawa gudanar da buda baki a cikin masallacin mai alfarma kamar yadda suka saba gudanarwa a kowace shekara a wani mataki na tsananta zaluncinsu kan al'ummar palastinu mazauna wannan birnin mai alfarma, da kuma wurare masu tsarki da ke cikinsa, wadanda Allah Allah ya yi wa albarka.
1066099