Bangaren kasa da kasa, buga wani kur'ani da aka yi da shafukansa ked a launuka ya jawo hatsaniya tsakanin wahabiyawan Saudiyya duk kuwa da cewa tare da sanin gwamnatin kasar da kuma amincewar ma'aikatr kula da harkokin addini ta kasar aka tsara sjhi kuma aka buga shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar sharq ausat da ake bugawa a birnin Riyad, cewa buga wani kur'ani da aka yi da shafukansa ked a launuka ya jawo hatsaniya tsakanin wahabiyawan Saudiyya duk kuwa da cewa tare da sanin gwamnatin kasar da kuma amincewar ma'aikatr kula da harkokin addini ta kasar aka tsara sjhi kuma aka buga shi, amma wasu daga cikin malamn wahabiyawa sun nuna rashin amincewa da hakan, tare da bayyana si da cewa ya saba wa sunna.
Gwamnatin wahabiyawan kasar Saudiyya tana taka gagarumar rawa wajen ganin ta samu karbuwa a siyasace a cikin kasashen musulmi da na larabawa musamman a yankin gabas ta tsakiya, inda take yin amfani da addini wajen cimma hakan, domin ta samu dammar aiwatr da siyasarta ta kare manufofin turawa a yankin da kuma kan kasashen musulmi da na larabawa, duk kuwa da cewa ya zuwa da dama daga cikin al'ummomin muslmi da na larabawa sun farka dangane da hakan.
Rahoton ya kara da cewa a wani bangare kuma za a gudanar da wani taro na girmama wadanda suka gudanar da hidima ta musamman ga kur'ani mai tsarkia garin Jidda da ke kasar Saudiyya kamar dai yadda majiyoyin kasar suka sanar musamman bangaren kula da harkokin kur'ani a ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar wadda kuma babban jami'in kula da harkokin liken asiri yana sanya ido matuka kanta da ayyukan da take gudanarwa, ta yadda ba zai yi hannun riga da siyasar kasar ba, musamman kan manufofin turawan yamma.
1065988