IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Ta Daliban Jami’a Musulmi Tana Kara Fito Da Matsayin Addini

16:35 - July 31, 2012
Lambar Labari: 2382267
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin mahalarta taron gasar karatun kur’ani ta duniya da ta kebanci daliban jami’oi na kasashen musulmi ya bayyana cewa gudanar da irin wannan gasa yana da matukar muhimmanci wajen kara fadadawa da daukaka matsayin Musulunci da kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin mahalarta taron gasar karatun kur’ani ta duniya da ta kebanci daliban jami’oi na kasashen musulmi ya bayyana cewa gudanar da irin wannan gasa yana da matukar muhimmanci wajen kara fadadawa da daukaka matsayin Musulunci da kur’ani mai tsarki a idon duniya.
Ya ci gaba da cewa kasashen musulmi ya zama wajibi kansu da su bayar da gudunmawa a dukkanin bangarori na addini da hakan ya hada da bangaren kur’ani mai tsarki, ta hanyar shirya gasa da kuma gayyatar daliban kur’ani daga sassa na kasar domin a raya shi, idan kuma ya kasance kasar tana da iko tana iya shiryawa a matsayi na kasa da kasa.
Muhammad Khazali daya daga cikin mahalarta taron gasar karatun kur’ani ta duniya da ta kebanci daliban jami’oi na kasashen musulmi ya bayyana cewa gudanar da irin wannan gasa yana da matukar muhimmanci wajen kara fadadawa da daukaka matsayin Musulunci da kur’ani mai tsarki ga sauran kasashe da al’ummomi.
1055529


captcha