IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Kara Tsananta Hare-Harensu A kan Masallacin Qods

16:35 - July 31, 2012
Lambar Labari: 2382269
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya sun kara tsananta harin ta’addancinsu kan masallacin Qods da kuma al’ummomin da suke rayuwa wuri na palastinawa bisa abin da ake zaton cewa yunkuri na hana gudanar da taruka na ranar Qods kamar yadda aka saba a kowace shekara.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa yahudawan sahyuniya sun kara tsananta harin ta’addancinsu kan masallacin Qods da kuma al’ummomin da suke rayuwa wuri na palastinawa bisa abin da ake zaton cewa yunkuri na hana gudanar da taruka na ranar Qods kamar yadda aka saba a kowace shekara a palastinu da sauran kasashen duniya.
A wani labarin na daban kuma shugaban kasar Iran dakta Mahmoud Ahmadinejad ya ce Iran za ta iya kawo wa kasuwar hada-hadar danyan man fetur ta duniya cikas matukar dai kasashen Yamma suka ci gaba da yin amfani da siyasa wajen shata farashin mai sabanin barin sa kamar dai yadda farashin kowace haja ke hawa ko kuma sauka daidai bukatar kasuwa. Shugaba Ahmadinejad ya bayyana hakan ne a safiyar yau lokacin da yake kaddamar da wasu kamfanonin hakowa da kuma tace man fetur guda biyu a nan Iran, yana mai cewa a matsayin Iran na kasar da ke samar da kaso mai tsoka a kasuwar danyan mai ta duniya, ba ta yadda kasar za ci gaba da zura ido wasu na shata farashin mai akan manufofi na siyasa, kuma domin ganin cewa an samar da gyara a wannan bangare, Iran a shirye take ta dakatar da samar wa kasuwar da mai domin kare wannan manufa.
Ahmadinejad ya jinjina wa manyan injinoyi na kasar da suka taka gagarumar rawa wajen tafiyar da illahirin cibiyoyi masu gudanar da ayyukan man fetur na kasar, wadanda kafin nasarar juyin juya halin musulunci suka kasance Turawa da kuma Amurkawa ne ke tafriyar da su.
1065747

captcha