Bangaren kasa da kasa, muslmin kasar Afirka ta kudu sun nuna rashin amincewarsu da matakain da ake shrin dauka a kasar na cire alamar hall a kan abinci wanda musulmi suke amfani da shi a matsayin abincinsu wanda yahudawa da mabiya addinin Hindus suke ta kokarin sukarsa.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam, cewa muslmin kasar Afirka ta kudu sun nuna rashin amincewarsu da matakain da ake shrin dauka a kasar na cire alamar hall a kan abinci wanda musulmi suke amfani da shi a matsayin abincinsu wanda yahudawa da mabiya addinin Hindus suke ta kokarin sukarsa domin kawo rikici tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba.
Dangane da kasar Kenya kuwa za’a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki a kasar a cikin watan Marsi na shekara mai zuwa. Wata kotun daukaka kara a kasar ce ta yanke wannan hukunci, wanda tabbatarwa ne ga hukuncin da wata karamar kotu ta yanke a cikin watannin baya. Daya daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil’adama, wadanda suke bukatar a gaggauta gudanar da zaben, ta bayyana cewa zata sake daukaka kara kan wannan hukuncin.
Zaben na watan maris mai zuwa dai zai zama zabe na farko tun bayan wanda ya jawo tashen tashen hankula a kasar a shekara ta 2007, inda fiye da mutane 1,220 suka rasa rayukansu a ricikin da ya biyu bayan zaben. Hudu daga cikin alkalai 5 da suka yanke wannan hukuncin a yau dai, sun bukaci a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 4 ga watan Maris kamar yadda hukumar zaben kasar ta tsara. Zaben har ila yau shi ne na farko tun bayan an amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar.
1067349