IQNA

An fara Gudanar Da Gasar Karatun Kur’ani Mai tsarki Ta Kasar Gunea Konakry

17:34 - August 01, 2012
Lambar Labari: 2383339
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Gunea Konakry a karo na talatin da biyu da aka saba gudanarwa a kowace shekara tare da halartar makaranta da mahardata da sassa na kasar da kuma wasu yankuna nakashe da ke makwabtaka domin raya wannan wata mai albarka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na radio-kankan, cewa an fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Gunea Konakry a karo na talatin da biyu da aka saba gudanarwa a kowace shekara tare da halartar makaranta da mahardata da sassa na kasar da kuma wasu yankuna nakashe da ke makwabtaka domin raya wannan wata mai albarka na ramadana mai alfarma.
Wani labarin kuma an kai harin bam a safiyar yau kan ginin sashen tara bayanan asiri na rundunar sojan kasar Libya da ke birnin Benghazi wanda shi ne cibiyar masu hamayya da mulkin kanar Kaddafi. Wani babban jami'i a rundar sojan kasar ta Libya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa cewa, maharan sun yi amfani ne da manyan bama-bamai wajen kai harin, wanda hakan ya yi sanadiyyar rugujewar wani bangare na ginin mai hawa biyu, sai dai bai bayyana adadin mutanen da suka rasu ko kuma suka samu raunuka sakamakon hakan.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun faruwar irin wadannan hare-hare a Benghazi da kuma sauran yankuna na kasar ta Libya ba, hare-haren da kuma ake dangantawa da kungiyoyin da suka yaki Kanar Kaddafi amma kuma a yau suke fada da yadda ake tafiyar da kasar ta Libya, wadda ta yi fama da rikici kuma take ci gaba da ganinsa tun bayan kisan gillar da yan tawaye suka yi wa tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar.
1067212


captcha