IQNA

Gasar karatun Kur’ani Mai Tsarki Ta Kasa Da Kasa A Pakistan A Cikin Wannan Wata

17:34 - August 01, 2012
Lambar Labari: 2383341
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarkia matsayi na kasashen duniya a kasar Pakistan kuma zaman taron wannan gasa ya gudana ne a birnin Islam abad fadar mulkin kasar tare da halartar wakilai daga cibiyoyin addinin muslumma na kur’ani da suke kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Times, cewa an gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarkia matsayi na kasashen duniya a kasar Pakistan kuma zaman taron wannan gasa ya gudana ne a birnin Islam abad fadar mulkin kasar tare da halartar wakilai daga cibiyoyin addinin muslumma na kur’ani da suke kasar wadda day ace daga cikin kasashen musulmi.
A wani rahoton kuma an bayyana cewa Lalacewar cibiyoyin bada wautan lantarki a kasar India a jefa fiye da rabin mutanen kasar biliyon 1.2 cikin duhu a yau talata. Yankewar wutan lantarkin ya rutsa da masu hakar ma’adianai a karkashin kasa, ya dakatar da zirga zirgan jiragen kasa da kuma jefa asbitoci da dama cikin duhu. Wannan dais hi ne lalacewar cibiyoyin bada wutan lantarki mafi muna wanda kasar ta fuskanta a fiye da shekaru guma da suka gabata. Katsewar wutan yan fara daga yankin Assam kusa da kasar China har zuwa yankin himalayar da kuma saharar Rajasthan .
Shugaban kamfanin bada wutan lantarkin kasar ta India. Nayak, ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa kafin ma su gano dalilin da suka jawo katsewar wutan a jiya litinin sai suka kara samun yankewar wutar a wasu Karin yankunan a yau talata. Ministan makamashin kasar ta India Sushilkumar Shinde, ya dora laifin katsewar wutan kan jihohin da suke zukar wutan fiye da yadda aka kayyada masu, wanda hakan ya jawo rikicewar tsarin rabon wutan. Fiye da mutane miliyon 670 a jihohi fiye da 12 ne katsewar wutan ya jafasu cikin duhu.
Masu hakar ma’adinin Coal kimani 200 ne aka rutsa da su a cikin rami a yammacin jihar Bengal a lokacinda injin lifata da ke jigilarsu ta tsaya cik. Wasu jami’an kamfanin hakar coal a gabacin kasar sun bayyana cewa masu hakar ma’adinai wadanda suke kimanin mita 700 a karkashin kasa a yankin dai basu shiga wani hatsari sanadiyyar rashin wutar ba. Jaragen kasa a garin kalata duk sun tsaida ayyukansu.
1066936
captcha