Bnagaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa kasar tana da bukatuwa zuwa makaman kungiyar domin kuwa akwai barazanar haramtacciyar kasar Isra’ila akanta wanda kuma rashin wadannan makamai babbar dama ce ga haramtacciyar kasar ta ci karen babu babbaka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din alamanar cewa, Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa kasar tana da bukatuwa zuwa makaman kungiyar domin kuwa akwai barazanar haramtacciyar kasar Isra’ila akanta wanda kuma rashin wadannan makamai babbar dama ce ga haramtacciyar kasar ta ci karen babu babbaka a lebanon da sauran kasashen yankin.
Babban sakataren kungiyar gwagwarmaya da HKI ta Hizbulla a kasar Lebanon Sayyeed Hassan Nasaralla ya bayyana cewa kasar Lebanon tana bukatar wanzuwar makamai a hannun kungiyar don kare kasar daga barazanar HKI. Sayyeed Nasarallah ya bayyana haka ne a jiya a wani jawabin da ya gabatar ta Vidio, a bakin cika shekaru 67 da kafa rundunar sojojin kasar Lebanon a Berut. Nasarallah ya zargi gungun jam’iyyun siyada ta “14-Maris” masu samun goyon bayan gwamnatocin kasashen yamma da kokarin takurawa kungiyar ta mika makamanta ga sojojin kasar.
Idan mun mika makaman mu ga rundunar sojojin kasar Lebanon kamar yadda wadannan jam’iyyu suke bukata, ina sojojin zasu ajiye makaman, don dai sojoji basa boye makamansu kamar yadda mu muke yi” inji shi. Sayyeed nasarallah ya ce kasshen Amurka da HKI sun fara bukatar kwance damarar kungiyar Hizbullah ne bayan korar sojojin HKI daga kudancin kasar a shekara ta 2000 da tayi.
1068184