Bangaren kasa da kasa, an bayyana dalilan da suka sanya aka dage taron fadakr musulmi da kuma batun palastinu a taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa da ke gudana a karo na ashirin da cewa bangaren hulda da jama’a na taron ne ba su bayar cikken hadin kai da ake bukata ba domin gudanar da taron.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na cikin gida, cewa an bayyana dalilan da suka sanya aka dage taron fadakr musulmi da kuma batun palastinu a taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa da ke gudana a karo na ashirin da cewa bangaren hulda da jama’a na taron ne ba su bayar cikken hadin kai da ake bukata ba domin gudanar da taron kamar yadda akasar da shiya shi.
Gamayyar kungiyoyin farar hula a kasashe musulmi ta WEA ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da wani mtum mai kiran kansa kirista ya yi a kasar Amurka da sunan fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi wanda gwamnatin Amurka da sauran gwamnatocin kasashen turai ba su uffan a kansa ba.
Wakilin musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Afghanistan ya bukaci da hukunta dukkanin wadanda suke da hannu a keta alfarmar kur’ani mai tsarki a kasar tare da kiran kungiyar tsaro da ta gaggauta yin hakan domin kawo karshen wutar rikicin da hakan ya jawo.
Jami’in ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Kabul na kasar, inda ya ce hakika abin da ya faru keta alfarmar kur’ani ne wanda kuma hakan ko shakka babu keta alfarmar duk wani musulmi ne aduniya, daboda hakan wadanda suka yi wannan mummunan aiki ne suke da laifi, kuma hukunta ne su kawai zai kawo karshen bala’in da hakan ya jawo a kan nato da dakarunta a kasar.
1068818