Bangaren kasa da kasa, gudanar da taruka na baje kolin kur’ani mai tsarki wata babbar dama ce ga musulmi masana da masu fasaha da su hadu domin nuna irin baiwar da Allah ya yi musu domin kara fito da matayin kur’ani mai tsarki a idon duniya kuma su san juna daga kasashen muuslmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da wani masani daga kasar Faransa Naman Zikri, ya bayyana cewa gudanar da taruka na baje kolin kur’ani mai tsarki wata babbar dama ce ga musulmi masana da masu fasaha da su hadu domin nuna irin baiwar da Allah ya yi musu domin kara fito da matayin kur’ani mai tsarki a idon duniya kuma su san juna daga kasashen musulmi da suke halartar taron.
Ya ci gaba da cewa kafin zuwansa wajen taron baje kolin kur’ani na kasa da kasa abirnin Tehran, yana da labarai kan Iran amma kuma abin mamaki shi ne, yadda dukkanin masaniyar da yake da ita ta hanyar labaran da yake ji ko yake karantyawa a jaridu, hakan ya yi hannun riga da abin da ya gani a kasar ta Irean, domin kuwa ya samu kasar a cikin natsuwa kuma kowa yana hidimarsa ba tare da wata tsangwama ba kamar yadda kafafen yada labaran turai suke ta yayatawa.
Ko shakka babu gudanar da taruka na baje kolin kur’ani mai tsarki wata babbar dama ce ga musulmi masana da masu fasaha da su hadu domin nuna irin baiwar da Allah ya yi musu domin kara fito da matayin kur’ani mai tsarki a idon duniya kuma su san juna daga kasashe daban-daban.
1069252