IQNA

Zanga-Zanga A Sassan Saudiyya Domin Nuna Rashin Amincewa Da Salon Mulkin Kasar

15:12 - August 03, 2012
Lambar Labari: 2384145
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane a sassan kasar Saudiyya sun gudanar da gangami da jerin gwano domin nuna rashin amincewa da salon mulkin zalunci da fir’ananci na mahukuntan kasar wadda ke yin dukaknin iyakacin kokarinta domin kare manufofin kasashen yammacin turai da kuma haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa dubban mutane a sassan kasar Saudiyya sun gudanar da gangami da jerin gwano domin nuna rashin amincewa da salon mulkin zalunci da fir’ananci na mahukuntan kasar wadda ke yin dukaknin iyakacin kokarinta domin kare manufofin kasashen yammacin turai da kuma haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin baki daya da kuma a cikin kasashen musulmi.
Shi kuwa a nasa bangaren Abdlmalik Husi joran mabiya Husi a yanin arewcin kasar Yeman ya bayyana cewa babban makiyin al’ummar musulmi a halin yanzu haramtacciyar kasar Isra’ila ce kuma ita ce hankoron ganin ta juya yunkurin da mutanre suke yi a cikin kasashen larabawa na neman samar da sauyi na adalci, zuwa ga manufarta da kuma yadda suke fatan ganin larabawa sun da gwamnatocinsu sun koma karkashinsu baki daya.
Ya kara da cewa gwagwarmayar musulunci ta koyar da haramtacciyar kasar Isra’ila babban darasi wanda ba za ta tabata manta da shi ba a cikin tarihinta kuma hakan ya sanya yahudawan sahyuniya sake tunani kan cewa za a iya lallasa su a hannun kungiyoyin gwagwarmaya masu tsarkakakkiyar zuciya da imani da Allah.
Kungiyar gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta hizbulla ta fitar da wani bayani da acikinsa take mayar da martani kan furucin sakataren majalisar dinkin duniya dangane da makaman kungiyar, inda bayanin ya ce hakkin lebanon ta mallaki makamai na gwagwarmaya domin mayar da martani kan wuce gonda irin yahudawan sahyuniya kan al’umma.
1069407



















captcha