IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Kira Da A rika Kare Hakkokin Musulmi Marassa Rinjaye

11:27 - August 06, 2012
Lambar Labari: 2386647
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kira a rika kare hakkokin musulmi marassa rinjaye a cikin sauran kasashen duniya musamman ma ganin yadda ake cin zarafin su a wasu kasashen saboda kasantuwar su mabiya muslunci ne kuma bugu da karui kan hakan bas u ne masu rinjaye ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC, cewa kungiyar kasashen musulmi ta yi kira a rika kare hakkokin musulmi marassa rinjaye a cikin sauran kasashen duniya musamman ma ganin yadda ake cin zarafin su a wasu kasashen saboda kasantuwar su mabiya muslunci ne kuma bugu da karui kan hakan bas u ne masu rinjaye ba kamar yadda yhakan ta faru a kasar Myanmar a cikin lokutan nan.

Kungiyar kasashen Musulmi ta OIC za ta tura tawaga ta musamman zuwa kasar Bama ko kuma Myanmar domin jin dalilan gwamnatin kasar na bayar da umurnin korar musulmi daga kasar. A lokacin da yake gabatar da jawabi ga mahalarta wani taro da kungiyar ta shirya a yau lahadi a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, Babban Magakatarda na Kungiyar Ekmaluddin Ihsa-noglu ya ce babbar manufar wannan tawagar da za a tura zuwa kasar ita ce tattaunawa da Hukumomin kasar kan yadda za a warware wannan matsala ta ruwan sanyi.

Su dai hukumomin kasar Myanmar sun bayyana cewa musulmin kasar 'yan kabilar Rohingya ba cikakken 'yan asalin kasar ba ne, saboda haka suka umurce su da su bar kasar, lamarin da kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 80, yayin da kungiyoyin kasa da kasa da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka rufe ido kan wannan abun assha da ke faruwa a kan musulmi

Rahoton ya kara da cewa taron kasa da kasa da aka gudanar a kasar Malesiya ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar musulmi a kasar Myanmar wato "Bama". Taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malesiya a jiya juma'a ya bayyana kisan gillar da ake yi wa musulmai a kasar Myanmar musamman a jihar Rakhine da cewar take hakkin bil-Adama ne da ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.

Daga cikin mahalarta zaman taron sun kuma bukaci daukan matakin matsin lamba kan gwamnatin Myanmar domin ta bada izini ga kungiyoyin kasa da kasa musamman kungiyar hadin kan kasashen musulmi don su kai taimakon gaggawa ga musulmin da suke cikin muwuyacin hali. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ce ta bukaci gudanar da zaman taron, kuma kungiyoyin kasa da kasa kimanin 30 ciki har da Majalisar Dinkin Duniya ne suka halacci taron na kasa da kasa.

Musulmi kasar Myamnar dai sun jima suna kokawa kan halin da suka kansu a ciki na zalunci da danniyar da ake nuna musu a kasar tsawon shekaru, mafi muni daga cikin abin da suka gani dai shi ne a cikin watan Yulin day a gabata.

1071535



captcha