IQNA

Kwamitin Alkalan Gasa Mai Karfi Da gogewa Yana Kara Armashin Gasar

11:27 - August 06, 2012
Lambar Labari: 2386648
Bangaren kasa da kasa, kwamitin alkalan gasar karatun kur'ani mai tsarki da ke gudanar da ayyukansa bias asasi na gogewa da cikakkiyar masaniya kan aikinsa yana bayar da karfin gwiwa ga makaranta da kuma masu halarta domin kallo ko kuma ta hanyoyin sadarwa domin hakan shi ne bababn abin ke kayatr da gasar a dukkanin bangarori.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar day a yi da daya daga cikin alkalan gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da kebanci Taliban jami'a, Abdulkadir Tarturi ya bayyana cewa kwamitin alkalan gasar karatun kur'ani mai tsarki da ke gudanar da ayyukansa bias asasi na gogewa da cikakkiyar masaniya kan aikinsa yana bayar da karfin gwiwa ga makaranta da kuma masu halarta domin kallo ko kuma ta hanyoyin sadarwa domin hakan shi ne bababn abin ke kayatr da gasar a dukkanin bangarorin gasar da ake samun bunkasarta a kowace shekara.

A wani labarin kuma daruruwan matasa a birnin Gao na Arewacin Mali sun hana wa 'yansandar zartas da shara'ar musulunci da ke birnin yanke hannun wata mata da aka ce wai ta sace bindiga kuma ya kamata a kire ma ta hannu a safiyar yau a wani dandali da ke tsakniyar birnin. Majiyoyi sun ce a cikin daren jiya ne masu kishin Islamar da ke iko da birnin suka fitar da wata sanarwar a kafafen yada labarai inda suka gayyaci jama'a da su taru a wani dandali da ke birnin domin su shaidi yadda za kira wa wannan mata hannu, to amma kafin ma 'yansandar zatas da shari'ar sun hallara tuni jama'a sun yi cikar kwari a dandali inda kuma suka hana a yanke wa matar hannu.

Daga bisani dai ala dole 'yansandar suka bar wurin ba tare da zartas da wannan hukunci ba, yayin da daruruwan matasan da ke wurin suka rera taken kasar Mali a matsayin samun galaba. A cikin makwanni biyu da suka gabata, jami'an kungiyar Mujao daya daga cikin kungiyoyi masu ra'ayin Islama da ke rike da yankin sun sanar da cewa sun kashe wasu mutane biyu mace daya da kuma namji daya ta hanyar jefe su da duwarwatsu a wani gari da ke karkashin ikonsu a cikin Arewacin kasar.


1068611
captcha